Kyama ga likitocin Ebola
December 20, 2014Majalisar ta yi kiran ne ga kasashen da ke fama da annobar cutar Ebola mai saurin kisa a yankin yammacin Afirka, inda ta ce likitocin na yin aiki tukuru domin ganin an kawo karshen cutar. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-moon ne ya yi wannan kira a yayin da ya isa kasar Guinea a rana ta biyu ta ziyarar da yake yi domin bayyana godiyarsa ga likitocin da ke kula da masu Ebolan a kasashen da cutar ta fi kamari. Kididdigar baya-bayan nan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar dai, ta nunar da cewa kawo yanzu mutane dubu 7,373 ne suka rasa rayukansu sakamakon Ebola a kasashe uku da cutar ta fi kamari a yankin yammacin Afirka. Ban Ki-moon dai ya fara ya da zango ne a Laberiya kafin daga bisani ya isa kasar Saliyo, inda a Asabar din nan ya isa kasar Guinea yayin da kuma zai kammala ziyarar ta sa a sansanin jami'an yaki da cutar Ebola na Majalisar Dinkin Duniya (UNMEER) da ke kasar Ghana bayan ya ziyarci kasar Mali.