Kyamar 'yan China na karuwa a dalilin Coronavirus
February 4, 2020
Akidar kyamar 'yan asalin kasashen Asiya na ci gaba da yaduwa a kasashen duniya tun bayan billar cutar Coronavirus a kasar Chaina inda yanzu adadin mutane da suka kamu da cutar ya habra dubu 20 a yayin da na wadanda suka mutu ya karu zuwa 425. Rahotanni daga Ostareliya na cewa wani marasa lafiya ya ki ya gaisa da wata likitarsa a bisa fargabar kamuwa da cutar ta Corona.
Jaridun kasar Italiya ma sun ruwaito a wannan Talata cewa jama'a a birnin Venise sun ta yi kaki kan rukunin wasu 'yan yawon buda ido 'yan kasar ta Chaina a birnin, a yayin da a birnin turin jama'ar unguwa suka zargi wasu iyalai 'yan asalin kasar Chaina da yada cutar ta Coronavirus.
A birnin Milan kuwa wasu iyaye mata ne suka yi amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen kira ga jama'a da su nisantar da 'ya'yansu daga 'yan asalin kasar Chaina su kuma nisanci shagunan 'yan Chaina. A kasar Malaisiya mutane kimanin dubu 500 suka sanya hannu kan wata takarda da ke kira da a dauki matakin haramta wa 'yan kasar Chaina shigowa kasar ta Malesiya baki daya.