Amirka ta karrama sojanta da ya mutu a Nijar
August 17, 2019Talla
An mika kyautar girmamawar, mafi girma da ake bai wa duk wani jami'i da ya mutu a fagen daga, ga iyalan mamacin a jihar Florida a yammancin ranar Juma'a. Mayakan jihadi fiye da dari ne suka yi wa Sajan Johnson da rundunar kawanya, a yayin da suke farautar wani jagoran kungiyar IS da ayyukansa suka addabi al'ummar yankin Afirka ta Yamma. Soji hudu ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin na wancan lokacin.