1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yulia Navalnaya za ta samu kyautar DW ta 2024

Abdourahamane Hassane
May 3, 2024

Matar marigayi madugun 'yan adawar kasar Rasha Alexei Navalny da gidauniyarsa mai yaki da cin hanci da rashawa sune suka lashe lambar yabo ta 'yancin fadin albarkacin baki na DW karo na 10.

Yulia Navalnaya
Yulia Navalnaya Hoto: Ebrahim Noroozi/AP/picture alliance

 Tashar DW za ta ba da kyautar 'yanci fadar albarkacin baki mai dakin dan adawar nan Navalny wanda ya mutu a gidan kurkuku a watannin da suka gabata, da kuma wata  kungiyar yaki da cin hanci da ke a Rashar ta Alexei Navalny  saboda fafutukar da suke yi na samar da demokaradiyya a Rashar. za dai a dai bayar da wannan kyauta a karo na 10 a ranar 5 ga watan Yuni a   Berlin.