Kyautar lambar yabo ga Merkel
November 18, 2010Shugaban Amirka Barak Obama ya ambaci sunan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin wadda za ta samu babbar lambar girmamawa akan 'yanci. Lambar yabon dai ita ce babbar karramawa da ƙasar Amirka ke yiwa farar hula. Merkel dai tana cikin jerin mutane 15 ɗin da shugaban na Amirka ya ambata sunayen su a matsayin waɗanda za su sami lambobin cikin wata sanarwar daya fitar a jiya Laraba.
Obama ya yi nuni da cewar Merkel ce mace ta farko kana ta farkon da ta fito daga yankin gabashin Jamus da ta ɗare bisa kujerar shugabancin gwamnatin ƙasar tun bayan haɗewar yankunan gabashi da kuma na yammacin Jamus. Sauran mutanen da za su ci gajiyar wannan karramawar a bana kuwa sun haɗa ne da tsohon shugaban Amirka George H. W. Bush, kana da wani mai zuba jari Warren Buffett sai kuma Marubuci Maya Angelou. A farko farkon shekara mai kamawa ne idan Allah ya kaimu fadar shugaban Amirka ta White House za ta shirya bukin miƙa musu lambobin girmamawar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas