1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru Awal AMA
December 13, 2019

Bikin ba wa Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed kyautar zaman lafiya ta Nobel ya dauki hankalin wasu daga cikin jaridun Jamus a sharhin da suka yi kan nahiyar Afirka.

Norwegen l Verleihung des Friedensnobelpreis an Abiy Ahmed in Oslo
Hoto: picture alliance/dpa/NTB scanpix/H. M. Larsen

A sharhin da ta yi jaridar Frankifurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa Abiy Ahmed ya dage kan ganin an samu hadin kan kasa bayan shekaru na rikice-rikice. Jaridar ta ce abi da ke faruwa a yankin Kahon Afirka na da tasiri har zuwa nahiyar Turai, domin babu wani yanki da 'yan gudun hijirarsa ke shigowa Turai da ya kai 'yan wannan yanki, sannan masu fashin teku a gabar tekun gabashin Afirka na zama masu hatsari ga sufurin daga Asiya zuwa Turai, kana kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabaab a Somaliya ta addabi yankin. Bugu da kari rigingimu na kabilanci da mulki na kama karya sun kara dagula lamura, misali rikicin tsakanin Habasha da Iritiriya da rikicin kan iyaka tsakanin Iritiriyar da Jibuti. Amma canjin shugabanci da aka samu a Habasha a watan Afrilun shekarar 2018, inda aka samu sabon Firaminista Abiy Ahmed, abubuwa sun dauki sabon salo na, abin da kawo karshen yaki tsakanin kasarsa da Iritiriya na tsawo shekaru 18, sannan ya dauki sahihan matakai da sukamkawo canje-canje masu fa'ida ga kasarsa.

Da sunan al'umma wannan shi ne taken sharhin da jaridar Süddeutche Zeitung ta yi kan kyautar zaman lafiyar da aka ba wa Abiy Ahmed. Ta ce Firaministan ya karbi kyautar da sunan al'ummar kasarsa da ta Iritiriya kamar yadda ya fada a jawabinsa. Jaridar ta ce ko shakka babu Abiy Ahmed ya taka rawar gani inda ya dinke barka tsakanin kasarsa da makwabciya Iritiriya sannan ya yi kokarin shiga tsakanin warware wata takaddamar tsakanin Iritiriya da Somaliya, to sai dai a watannin baya bayan tashe-tashen hankula sun karu a kasarsa, lamarin kuma da ya yi barazanar mayar da hannun agogo baya a yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma da kasar Iritiriya domin ya kai ga rufe kan iyakokin kasashen biyu.

Zaman kotun duniya kan laifukan yaki Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung labari ta buga game da zaman kotun duniya kan laifukan yaki, inda shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi wadda ta taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel ta kare matakan da sojojin kasarta suka dauka kan al'ummar Musulmin Rohingya, biyo bayan kararta da kasar Gambiya ta shigar a kotu da ke binin The hague an kasar Holland. Kasar Gambiya da ke yammacin Afirka ta yi karar cewa rundunar sojin Myanmar ta aika kisan kare dangi am kan Musulmin na Rohingya da nufin kawar da kawar da su gaba daya ko wani sashe na su daa doron kasa. Sai dai Aung San Suu Kyi da ta kare kanta a kotun ta ce sam babu zancen kisan kare dangi, amma a lokaci guda ta ce sojojin sun wuce gona da iri. Za a dauki lokaci mai tsawo kafin a yanke hukunci kan batun.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Dejong

Matsalar wutar lantarki a Afirka ta Kudu Matsalar karancin hasken wutar lantarki ta yi muni a Afirka ta Kudu inji jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung, tana mai cewa a farkon wannan mako kamfanin samar da wutar lantarki na kasar wato Eskom ya shiga mataki na shida na bayayyar wuta a kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka. Wannan matakin na nufin za a rage sama da akshi 15 cikin 100 na hasken wuatr lantarki da ake ba wa jama'a. Jaridar ta ce rashin gyara da ma sabunta injuna da sauran na'urorin samar da wuta na dag cikin dalilan da suka jefa Afirka ta Kudun cikin matsalar ta karancin wutar lantarkin.

Hoto: picture-alliance/Bildagentur-online/Schickert