Kyautar Nobel ta tattalin arziki
October 14, 2013Talla
Mutanen dai Eugene Fama,da Lars Hansen da kuma Robert Shiller dukkaninsu malaman jami'a ne a jami'ar Chigaco. Hukumatr ba da kyautar ta masauratar Sweden ta ce mutanen uku sun ƙware a kan wani tsarin da suka ƙirƙiro na yin hangen nesa na kasuwanin hada-hada da hanayen jari a cikin lokacin mai tsawo kamar shekaru uku zuwa biyar.
Kuma fusa'ar ta zama wani ma'auni ga masu saka jari a cikin ƙasashen duniya domin tantance yanayin saka jarin. Rober Shiller wanda shi ne ya fi yin suna a cikin su uku, ya fitar da wani mizani na frashin gidaje da sauransu wanda ake kira da sunan Case Shiler.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu