1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane biyu sun lashe kyautar Nobel

Zulaiha Abubakar
October 5, 2018

Kwamitin bayar da kyautar zaman lafiya ta Nobel Prize, ya mika kyautar bana ga wani likita dan kasar Kwango tare da wata 'yar fafutuka daga kasar Iraki, sakamakon yaki da cin zarafin mata a matsayin makamin yaki.

Bildkombo, Bildcombo  Dominique Gutekunst Denis Mukwege und Nadia Murad, Friedens-Nobelpreis 2018

Dr Denis Mukwege ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda aka ci zarafinsu yayin da Nadia Murad ta bayyanawa duniya irin yadda ta dandana kudarta a hannun 'yan ta'addan kungiyar IS. A lokacin mika musu wannan kyauta dai, kwamitin bayar da kyautar ya bayyana Dr Denis a matsayin jajirtacce wanda ya dade yana sukar gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da sauran kasashe kan rashin daukar matakin kawo karshen cin zarafin mata a matsayin makamin yaki, yayin da Nadia Murad ta kasance cikin mata 3,000 'yan kabilar Yazidi wadanda kungiyar IS ta yi awon gaba da su, kafin ta yi nasarar tserewa bayan watanni uku. Nadia dai  ta rubuta littafi kan halin da ta tsinci kanta yayin da take hannun 'yan IS din. Tuni dai gwamnatin kasar Kwango ta taya Dr Denis murna kan wannan ci-gaba da ya samu a rayuwarsa.