Labaran Afirka da ke jaridun Jamus
March 24, 2023Bari mu fara da jaridar Zeit Online: cikin sharhinta mai taken: Mutane na wantagaririya a Chimwankhunda da ke Blantyre, sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a ranar 14 ga wannan wata na Maris da muke ciki. Jaridar ta ce ambaliyar ruwan sama da aka samu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Freddy a kasashen Malawi da Mozambik, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Guguwar dai ta afku a karo biyu a kasa da makonni uku, inda masu aikin ceto ke gargadin cewa akwai fargabar adadin wadanda suka rasa rayukansu ka iya karuwa.
Mahaukaciyar guguwar da ta afku a yankin kudancin Afirka ta fara kamari tun a karshen mako, inda gwamnatin Malawi ta ce kimanin mutane 190 ne suka halaka yayin da wasu 584 suka jikkata kana wasu 37 suka yi batan dabo. Ita kuwa makwabciyar kasa Mozambique ta bayyana cewa mutane 20 ne suka halaka yayin da wasu 24 suka jikkata. Adadin mutanen da suka halaka a Malawi sakamakon mahaukaciyar guguwar ta Freddy dai, ka iya karuwa zuwa sama da 1000 kasancewar bala'in mahaukaciyar guguwar na karuwa kuma hakan na bai wa jami'an agaji wahalar aikin ceto. Rahotanni sun nunar da cewa zai wahala a samu damar ceto karin wasu mutane da ke raye.
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta nata sharhin mai taken: Auren jinsi a matsayin laifi a Yuganda, majalisar dokokin kasar ta amince da dokar haramta mu'amalar jinsi guda. Ta ce a Yuganda majalisar dokokin kasar ta amince da doka mai tsanani a kan masu mu'amalar jinsi guda da kuma wadanda ke sauya jinsinsu, inda wadanda suka yi aure ko suka yi amfaani da yara kanana za su fuskanci hukuncin kisa. A Talatar da ta gabata ne dai, majalisar ta amince da wannan doka, kuma duk wanda aka kama da kokarin karya dokar ka iya fuskantar hukuncin daurin rai-da-rai.
Dokokin zamanin mulkin mallaka dai sun haramta mu'amala tsakanin jinsi guda, kana masu auren jinisi na fuskantar hukunci mai tsauri tsawon shekaru a kasar da ke gabashin Afirka. Sabuwar dokar za ta fara aiki, da zarar Shugaba Yoweri Museveni na Yugandan ya rattaba hannu a kanta. Cikin dokar dai, duk wani wanda ya bayyana kansa da dan kungiyar masu auren jinsi ka iya fuskantar daurin shekaru 10 a gidan kaso. Sai dai duk da yadda wasu 'yan majalaisar ke bayyana amincewa da dokar domin kare addini da al'ada, wasu tsiraru cikinsu na ganin cewa ta saba da dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta bayyana Yuganda a matsayin kasa ta farko a Afirka da ta amince da irin wannan doka koda yake an haramta auren jinsin a sama da kasashen Afirka 30.
Ita kuwa jaridar die Tageszeitung labari ta buga dangane da gangamin adawa da masu fafatuka suka kira a manyan biranen Afirka kama daga Nairobi zuwa Pretoria dangane da tsadar rayuuwa da haihawan farashi.
Jaridar ta ce hakika an gudanar da zanga-zanga a kasashe da dama a ranar Litinin. Lamarin dai ya fi kamari ne a kasar Kenya, inda ake nuna bacin rai game da hauhawar farashin kayan abinci da kuma fushin 'yan adawa kan nasarar da shugaba William Ruto ya yi a zaben da ya gabata.
An yi ta gwabza fada a titina a tsawon yini a wasu sassan babban birnin kasar, Nairobi, inda masu zanga-zangar suka nemi yin kunnen uwar shegu da kiran da 'yan adawa karkashin jagorancin madugun 'yan adawa Raila Odinga, suka yi na yin tattaki zuwa gidan gwamnati.