1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Labaran karya na yaduwa a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
January 2, 2020

Kasashen Afirka da dama sun yin kaurin suna a fuskar yada labaran kanzon kurege da nufin cimma buri na kashin kai. Kafofin sada zumunta na zamani sun taimaka wajen yada labaran karya a Kamaru da Ghana da Afirka ta Kudu.

Social Media-Nutzung in Afrika
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Yanzu haka dai ya zama al'ada a kasar Kamaru a kowanne mako a sami bullar sabon labarin bogi, wanda kuma sai bayan ya dauki hankalin al'umma kafin a san cewar ba sahihin labari ba ne. Al'umma sun dora alhakin bazuwar irin wadannan labaru a kan shafukan sadarwar na zamani.

A Afirka ta Ludu ma, labaran bogi sun zama gama gari a 2019 saboda kafofin sada zumunta na zamani sun zama hanya mafi sauki na samun labarai cikin sauki, ko da yake su ne jigon yada labaran karya.

Batun yada jita-jita ya dade yana wakana a kasar a kasar Ghana. Amma  jama'a na cewa zuwan shafukan intanet ya habbaka wannan dabi'a, inda yanzu bambance labarin gaskiya da na karya ke zama jidali ga 'yan kasar.