Labarin Wasanni: 02.03.2026
March 2, 2026
Shirya gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata na ci gaba da zama karfen kafa ga CAF da ke zama hukumar tamaula ta wannan nahiya saboda rashin tabbacin samun kasa da za ta dauki bakunci. Bayanai da kafar watsa labarai ta Sports News Africa ta wallafa, sun nunar da cewar za a iya dage gasar da aka shirya farawa a ranar 17 ga Maris bayan da Maroko ta nuna wannan bukata tun makonnin da suka gabata, duk da fice da ta yi waje daukar bakuncin gasar matan Afirka sau biyu a cikin tarihi.
Sai dai duk da kokarin da Hukumar Kwalon Kafar Afirka ta yi zawarcin kasashe da dama ciki har da Afirka ta Kudu domin su maye gurbin Maroko, haka ba ta cimma ruwa ba domin Pretoria ta fara amincewa kafin ta lashe amanta. A halin yanzu dai, CAF ba ta fitar da lokacin da za a gudanar da gasar kwallon mata ba, lamarin da ke zama kalubale saboda gasar ce za ta tantance kasashen da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar duniya ta mata da za ta gudana a kasar Brazil a 2027.
Kungiyoyin mata na kasashen da suka cancanci shiga gasar sun tabbatar da burinsu na ganin su taka rawa, inda Côte d' Ivoire ta doke Jamhuriyar Benin da ci 2-1, yayin da Namibiya ta samu nasara a kan Afirka ta Kudu da ci 2-1. A nata bangaren Ghana ta mamaye Hong Kong da ci 4-0, yayin da Aljeriya ta tuntsurar da Masar da ci 3-0. Ita kuwa Indomitable Lionesses ta Kamaru ta yi nasara a kan Super Falcons ta Najeriya da ci 1-0 a wasan sada zumunta da aka yi a filin wasan soji na Yaounde babban birnin kasar a ci gaba da shirye-shiryen a gasar cin kofin Nahiyyar Afirka na 2026. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan matan Kamaru suke samun koma baya idan aka danganta da baya, kamar yadda wakilinmu Zakari Sadou ya ruwaito mana daga Douala.
A Spain kuma, matsalar wariyar launin fata ta haifar da tasgaro a mako na 25 na La Liga, lamarin da ya kai ga dakatar da wasa tsakanin Elche da Espanyol Barcelona na dan lokaci a ranar Lahadi bayan da dan wasa Omar El Hilali da ke da asali da Maroko ya yi korafin cewa abokin hamayyarsa Rafa Mir ya ci masa zarafi. Saboda haka ne alkalin wasa Iosu Galech Apezteguia ya yi amfani da tsarin yaki da wariyar launin fata a minti na 80 wajen dakatar da wasa.
Idan dai an samu Rafa Mir da wannan laifi, zai iya fuskantar hukunci mai tsanani. Amma La Liga ta mayar da martani a shafukan sada zumunta ba tare da ambaton wannan wasan kai tsaye ba, tana Allah wadai da "duk wani abin da ya danganci wariyar launin fata" a filin wasa ko a wajensa. Duk da kokarin hukumomi da kuma hukunce-hukuncen kotu kan wannan matsala, amma har yanzu fagen kwallon kafar Spain ta kasa kawar da wariyar launin fata a filayen wasa.
A nan gida Jamus, dan wasan baya kuma kyaftin na Borussia Dortmund Emre Can, ya samu rauni a gwiwarsa ta hagu a ranar Asabar a lokacin da ya yi karo da Konrad Laimer a minti na 38 a wasan el classico da Bayern Munich, lamarin da zai kai shi ga yin jinyar watanni da dama.
Wannan mummunan labarin ya zama wa Yaya-karama Dortmund goma da gomammiya saboda Yaya-babba Bayern Munich ta bita har gida kuma ta doke ta da ci 3-2 tare da samar da ratar maki 11 da mai biya mata baya a daidai lokacin da ya rage wasanni goma a Bundesliga. Wannan ne nasara ta 20 da Bayern ta yi a bana, wacce ta kai ga fara jin kamshin kambun zakara na bbaban lig na Jamus wanda zai zama na 35 a gare ta.
Ita kuwa Stuttgart ta yi nasarar dole Wolfsburg da ci 4-0 a gida, lamarin da ya bata damar daidaita yawan makinta 46 da Hoffenheim da ke a matsayi na uku, yayin da sauran wasanni goma suka rage a kakar wasa ta Bundesliga. A Bangarenta, RB Leipzig ta hambarar da Hamburg da ci 2-1, kuma ta ci gaba da kasancewa a matsayi na biyar, yayin da Bayer Leverkusen ta yi kunnen doki da Mainz, sakamakaon da zai kara matsa mata lamba a fafatawar da za ta yi a Hamburg a ranar Laraba idan tana so a dama da ita a gasar zakarun Turai a badi.
Dan tseren keke na kasar Jamus Moritz Kretschy, mai shekaru 23 ya lashe gasar Tour du Ruwanda ta 2026 a ranar Lahadi, inda ya kammala matakai takwas da su kunshi hawan dutse da sauran su. Wannan dai shi ne karo na uku da Kretschy, ke fafatawa tseren keke na Tour du Rwanda ta uku, kuma zama dan Turai na uku da ya lashe gasar , bayan dan tseren Spain Cristian Rodriguez a 2021 da dan Faransa Fabien Doubey a 2025.
A bangaren 'yan tseren keken Afirka kuwa, Henok Mulubrhan na Iritiriya ne kawai tauraronsa ya haska, inda ya samu nasara a mataki na 8 mai tsawon kilomita 83.8 a kusa da birnin Kigali. Dama dai Mulubrhan mai shekaru 26, ya taba lashe gasar Tour du Ruwanda ta 2023. 'Yan tsere da suka halarta daga kasashe tara sun hada da Jamus da Faransa da Burtaniya da Iritiriya da Spain da Ruwanda da Afirka ta Kudu da Amurka da kuma Maroko.