1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 04.07.2022

Mouhamadou Awal Balarabe M. Ahiwa
July 4, 2022

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi a Côte d' Ivoire a damuna ya sa CAF ta dage gasar kwallon kafa ta Afirka daga 2023 zuwa 2024. 'Yan matan Kamaru sun taka rawa.

Patrice Motsepe
Shugaban hukumar CAF, Patrice MotsepeHoto: Weam Mostafa/Sports Inc/empics/picture alliance

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka ta dauki matakin da aka dade ana jira na dage gasar cin kofin nahiyar na maza na gaba zuwa watanni Janairu da Fabrairu na shekarar 2024 maimakon watannin Yuni da Yuli na 2023. Shugaban CAF Patrice Motsepe da kansa ne ya yi wannan sanarwa a karshen taron kwamitin zartarwa na CAF a ranar Lahadi a birnin Rabat na kasar Maroko. Babban dalilin da Motsepe ya bayar shi ne yanayin damuna da ke hadassa ruwan sama kamar da bakin kwarya a Côte d'Ivoire a bazara wanda ka iya dakushe armashin gasar. Wannan dai shi ne karo na biyu da gasar za ta gudana a farkon shekara maimakon lokacin bazara baya ga wacce ta gudana a Kamaru a bana, lamarin da zai haifar da takun saka da kungiyoyin kwallon Turai wadanda ke jan kafa wajen barin 'yan wasan Afirka domin su je su buga wa kasashensu na asali.

'Yan matan Afirka na taka leda a gasar kwallon kafa ta mataHoto: Sydney Mahlangu/BackpagePix/empics/picture alliance

A bangaren mata, shekaru biyu bayan dage gasar kwallon kafar nahiyar Afirka sakamakon annobar corona, Maroko na daukar bakuncinta a karon farko cikin tarihin wannan kasa ta Maghrib. Wannan dai shi ne karo na 13 da AFCON ta mata ke gudana a Afirka tsakanin kasashen 12, kuma sanin kowa ne cewa 'yan mata Najeriya ne ke karyawa inda ba gaba sakamakon lashe kofuna 11 da suka yi.  A rukuni na biyu, Tunisiya ta doke Togo 4:1, yayin da Kamaru da Zambiya suka tashi ba wanda ya ci wani. A yanzu dai Tunisiya na kan gaba a wannan rukuni da maki 3. A rukunin farko kuwa 'yan matan Senegal sun doke na Yugnda da ci 2:0.  Su kuwa 'yan matan Maroko sun lashe wasan farko da ci 1-0 a kan takwarorinsu na Burkina Faso a gaban dubban 'yan kallo da suka shaidar da bikin bude gasar.

Jared Cannonier, wanda Israel Adesanya ya lallasa a Las VegasHoto: John Locher/AP Photo/picture alliance

Zakaran damben boxing na UFC na duniya ajin masu matsakaicin nauyi Israel Adesanya na Najeriya, ya doke Ba’amirke Jared Cannonier a Las Vegas, lamarin da ya sa shi zama gagarabadau a wannan fannin. Wannan ne dai nasara ta 12 a jere a gasar UFC a Adesanya ya yi a ajinsa, wanda ya sanya har yanzu ba a taba ganin zakara irin sa ba na tsukin kusan shekaru uku. Bakunan daukacin alkalan damben ya zo daya a ranar Asabar a kan nasarar Adesanya, duk da karfin da abokin hamayyarsa ke da shi saboda ya taba karawa a ajin masu nauyi kafin ya dawo ajin masu matsakaicin nauyin. Hasali ma dan damben na Afirka mai tsawon mita 1.93m, ya yi amfani da kafofinsa wajen taka rawar gani a zagaye biyar da aka yi,  ya Allah saboda kwarewa da yake da ita a fannin kick-boxing. 

'Yan dambaen gargajiya lokacin wasa a Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Shahararrun 'yan kokowa hudu na Jamhuriyar Nijar da zaratan 'yon kokowa hudu na Senegal su fafata a wata gasa da ta gudana daga ranar Jumma'a zuwa Lahadi a birnin Yamai. Sai dai a karshen kasar Senegal ce ta yi nasara inda ta samu nasara biyu da kunnen doki daya, yayin da Jamhuriyar Nijar mai masaukin baki ta samu nasara daya. Sai dai an samu tsaiko a gasar, inda sarkin 'yan kokawa na Nijar Issaka Issaka ya ki shiga kokawar a bisa wasu dalilai da suka jawo cece-kuce, na zargin shirya masa makarkashiya a filin kokawar saboda ya zama gagarabadau. Tsohon sarkin kokowar kasar Nijar Bala Harouna da sarkin kokowar Senegal na yanzu Ngom, su ne suka shirya gasar da ke zama irinta ta farko da ta taba hada 'yan kokowar kasashen biyu da sunan karfafa zumunta da hulda tsakaninsu.