1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal ta lashe kofin gasar CHAN

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
February 6, 2023

Senegal ta bai wa marada kunya a CHAN inda ta lashe kofin bayan da ta doke Aljeriya mai masaukin baki a bugun fenareti.

Senegal ta lashe gasar CHAN
Senegal ta lashe gasar CHANHoto: AFP

Shekara guda bayan nasarar Sadio Mane da sauran abokan wasansa a gasar AFCON ko CAN, Senegal ta  lashe kofin kwallon kafa na 'yan wasan Afirka da ake bugawa a gida, inda a ranar Asabar da ta gabata, ta shammaci Aljeriya mai masaukin baki, wacce kuma aka yi hasashen za ta kai labari. Hasali ma dai, bayan wasan na mintunan 90 wadanda damarmaki suka yi karanci, a bugun fenareti kamar yadda ya wakana a gasar AFCON na Kamaru ne, Les Lions de la Teranga suka zura kwallaye biyar a raga yayin da Aljeriya ta tashi da hudu. Kocin Senegal Pape Bouna Thiaw ya ce, aiki tukuru da daukacin masu ruwa da tsaki suka yi a fanninn kwallon kafa na tsawon shekaru goma ne suka fara girba a yanzu.

Sai dai shan kashi da Aljeriya ta yi, ya bakanta zukanta 'yan wasanta, wadanda suka taka rawar gani a gasar ta CHAN amma rashin sa'a ta sa suka baras da bugun daga kai sai mai tsaron gida. Ko da koci Aljeriya Madjid Bougherra, sai da ya nuna takaicinsa tare da yaba wa 'yan wasansa. Wannan shi ne rashin nasara na uku na Aljeriya a cikin shekara guda, baya ga rashin cancantar shiga matakin karshe na AFCON ko CAN da rashin cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

Fafatawar Aljeriya da Nijar a gasar CHANHoto: Wu Tianyu/IMAGO

A Jamhuriyar Nijar kuwa, tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar ta MENA da ta wakilci Nijar a gasar kwallon kafa ta ‘yan wasan da ke bugawa a gida wato CHAN ta koma gida bayan da ta samu matsayi na hudu. Baya ma ga tukuici mai tsoka da hukumomin kasar suka tadanar musu, 'yan wasan sun samu kyakkyawan tarbe daga daruruwan ‘yan kasar a lokacin komawar ‘yan wasan a gida bisa rabarrukin mai horaswarsu Harouna Doulla.

Kungiyoyin Al-Hilal na Saudiyya da Al Ahly ta Masar sun tsallake zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya na kungiyoyi da ke gudana a kasar Maroko. Ita dai Al-Hilal ta Saudiyya ta kawar da Wydad Casablanca da ke rike da kofin zakarun Afirka da ci 5- 4 a Rabat, yayin da a nata bangare, Al Ahly ta Masar ta doke tawagar Amirka Seattle Sounders da ci 1-0 a Tangier.

Harry KaneHoto: Nick Potts/PA Images/imago images

A Ingila, sakamakon zura kwallo a ragar Manchester City (1-0) da ya yi a ranar Lahadin da ta gabata a wasanni mako na 22 na Premier League, Harry Kane ya sa Tottenham samun nasara mai matikar daraja saboda ya zama dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihi. Wannan nasarar ta sa Tottenham cike gibin da ke tsakaninta da Newcastle, a kokarinta na cancantar shiga gasar zakarun Turai. Sannan ta kyautata matsayin jagoran Arsenal, wacce aka doke Everton (1-0) amma take ci gaba da yi wa Manchester City da ke a matsayi na biyu ratar makii biyar.

A nan Jamus, an gudanar da wasannin mako na 19 a gasar Bundesliga, inda dukkan kungiyoyi da ke saman teburi suka kai labari ciki har da Union Berlin da Borussia Dortmund da Yaya-babba Bayern Munich. Bayan wasanni uku ba tare da samun nasara ba, Bayern Munich ta farka daga barci inda ta lallasa Wolfsburg da ci 4-2. Duk da cewa 'yan wasan Bavaria sauki sun jijjiga bayan korar Joshua Kimmich a minti na 54, nasarar ta ba su damar kasancewa a kan gaba da maki 40. A halin yanzu dai, Bayern Munich na da ratar maki a kan Union Berlin, wacce ta doke Mainz da ci 2-1. Jordan Siebatcheu ne ya zura kwallo na biyu mai mahimmanci a minti na 84 da fara wasa.

Dortmund ta llalasa Freiburg da ci 5-1Hoto: Anke Waelischmiller/Sven Simon/picture alliance

Ita kuwa Borussia Dortmund da ta fara wannan shekara ta 2023 da kafar dama tana ci gaba da karyawa inda ba gaba, inda ta lallasa SC Freiburg da ci 5-1. Ga Edin Terzic, kocin Borussia, kungiyarsa ta gabatar da mafi kyawun wasanta na kakar wasa. ita kuwaa Eintracht Frankfurt wacce ta ya wa Hertha Berlin dukan kawo wuka 3-0 tana nan a matsayi na biyar da maki 35. Hasali ma dai, wannan nasarar Eintracht Frankfurt ya dagula wa Hertha Berlin lissafi domin ta kasance a matsayi na 17, lamarin da ya sa, sannu a hankali Schalke 04 ta fara murmurewa, inda ta yi wasanta na biyu ba tare da an doke ta ba,  0-0 da Borussia Monchengladbach

A sauran sakamakon kuwa, Bayer Leverkusen ta sake faduwa, a wannan karon a gaban Augsburg da ci 1-0. A yanzu dai 'yan wasan koci Xabi Alonso sun makale a tsakiyar teburi a matsayi na 10. Ita kuwa ta dare matsayi na 13, amma laya ta kasa yi wa Hoffenheim kyau rufi saboda Bochum ta lallasa ta da ci 5-2, kuma ba ta ci nasara ko daya ba a 2023. A yanzu dai tana tafiya kafada da kafada da Bochum a yawan maki 19 kowaccensu. Kungiyar Stuttgart ma na ci gaba da kasancewa cikin halin gaba kura bayan da Werder Bremen ta daka ta da ci 2-0  kuma ta kasance a matsayi na 16, Werder Bremen kuwa ta koma matsayi na 8.