1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 06.10.2025

October 6, 2025

Wasannin sun hada da karawa a gasar Bundesliga da yadda Arsenal ke jan zare a wasannin Premier na Ingila da La Liga da wasannin neman gurbin gasar kwallon duniya da ma wasu wasannin Premier ta Najeriya.

Harry Kane, dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich lokacin karawa da Bremen
Harry Kane, dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich lokacin karawa da BremenHoto: Matthias Schrader/AP Photo/picture alliance

Za mu faro da wasannin Bundesligar Jamus, inda a karshen makon jiya aka yi gumurzu a filayen wasanni daban-daban a mako na shida na kakar Bundesliga ta bana.

A wasannin da aka buga, FC Köln na ci gaba da yin abin kai inda ta bi Hoffenheim har gida ta doke ta ci 1-0, Augsburg ta doke Wolfsburg ci 3-1, Weder Bremen ta yi nasara a kan FC St Pauli ci 1-0, RB Leipzig ta taka wa yaya karama Borussia Dortmund birki a gidanta inda suka tashi kunnen doki 1-1, yaya babba Bayern Munich ta bi Frankfurt har gida ta laka mata duka ci 3-0, Bayern Leverkusen ta fara fardo da ruhinta inda surfa Union Berlin ci 2-0, wannan wasa ne ma muka kawo muku sharhinsa kai tsaye daga nan sashen Hausa na DW a maraicen Asabar

A sauran wasannin kuwa Stuttgart ta doke Heidenhein ci 1-0, Hamburg ta yi wa Mainz dukan kawo wuka ci 4-0, sai 'yar baya ga dangi B.Mönchengladbach ta yi canjaras da Freiburg ba tare da kowanen su ya zura kwallo ba.

Bayern Munich ce ke ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 18, yayin da B.Dortmund ke biya mata a matsayi na biyu da maki 14, RB Leipzig na a matsayi na uku da maki 13, Leverkusen ta tashi daga matsayi na bakwai zuwa matsayi na biyar da maki 11 yayin da FC Köln ta dare matsayi na shida da maki 10 inda ta shiga gaban Frankfurt mai maki tara. 'Yan baya ga dangi su ne Mainz da ke a matsayi na 16 da maki 4 yayin da B.Mönchengladbach da Heidenheim ke a matsyi na 17 da na 18 kowannen su da maku uku.

Hoto: Martin Agüera/kolbert-press/IMAGO

A Liga ta kasar Spain wasan mako na takwas ya birkitawa Barcelona lissafi bayan ta sha kashi a hannun Sevila ci 4-1. Wannan rashin nasara na biyu a jere da Tawagar ta Blaugrana ta yi bayan PSG ta doketa a gasar zakatrun Turai ya sa ta koma matsayi na biyu da maki 19 yayin da babbar abokiyar hamayya Real Madrid ta dare kan teburin gasar da maki 21 bayan doke Villareal ci 3-1. Ita ma Atletico da Madrid ta gamu ta turjiya daga Celta Vigo idan suka tashi wasa ci 1-1.

Idan muka nufi Ingila an kammala wasannin mako na bakwai nba gasar Premier, inda Arsenal da ta fara kakar bana da kafar dama ta yi tumbuke LKiverpool daga kan teburin bayan nasarar da ta a kan Wast Ham ci 2-0 yayin Chelsea ta sandi Liverpool din ta doke ta ci 2-1. Ita kuwa Manchester United ta yi abin kai inda ta doke Sunderland ci 2-0, Manchester City ta bi Brentfort har gida ta doketa da ci 1-0. A wasu daga cikin sauran wasanni na mako na bakwai na Premier Leeds United ta yi rashin nasara a gida a gaban Tottenham, Newcastel ta doke Nottingham Forest ci 2-0, Everton ta doke Crystal Palace ci 2-1, Aston Villa ta doke Burnley ci 2-1 sai kuma Walves da ta tashi kunnen doki Brighton ci 1-1.

A karshen wannan mako za a buga wasanni biyu na karshe da suka rage a neman gurbin zuwa gasar cin kwallon kafa ta duniya ta 2026. A nahiyar Afirka baya ga Moroko da Tunisia da tun tuni suka samu tikitensu, kasashen Masar da Aljeriya da kasar Cape Verde da Ghana na daf da bin sawusu yayin da harkoki suka sukurkurcewa tawagar Kamaru. Su kuwa kasashen Senegal da Cote d'Ivoir de kuma Benin sai sun yi da gaske kafin su samu na su tikiten yayin da Najeriya da Rwanda ka iya cin gajiyar hukuncin rage maki da hukumar FIFA ta yi wa Afirka ta Kudu.

Karawa tsakanin Maroko da Afirka ta KuduHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Wasu daga cikin wasanni da za su dauki hankali sun hada da karawa za a yi a ranar Laraba a tsakanin Jamhuriyar Afirka ta Tskiya – Ghana a rukunin I, Maurice – Cameroun a rukunin D, a ranar Juma'a Sudan ta Kudu za ta kara da Senegal a rukunin B, Seychelles da Cote d'Ivoire a rukunin F, Ruwanda da Benin a rukunin C, Lesotho da Najeriya a rukunin C, sai kuma Zimbabwe da Afirka ta Kudu a rukunin na C. 

Idan muka leka Najeriya gasar Premier na ci gaba da kankama inda hamayya ke kara zafi a tsakanin kungiyoyin da neman zama zakara, bayan kammala wasannin mako na bakwai. Babban abin da ya fara daukar hankali ma a Premier ta Najeriya shi ne yadda a gyara alkalkanci lamarin da ake gani ya taka rawa wajen samun nasarar da wasu kungiyoyi ke yi a waje.

Dan wasan Ingila Harry Kane ya sake kafa tarihi a kungiyar Bayern Munich inda ya zama da wasa na farko da ya zuwa kwallaye 11 a wasanni shida na farkon kakar Bundesligar Jamus. Kawo yanzu Harry Kane mai shekaru 32 ya ci wa Bayern Munich kwallaye daya-daya har 18 a wasanni 10 da ya buga a kakar bana, lamarin da ke nuna cewa dan wasan na a kan ganiyarsa.

A daidai lokacin da komai ke raya wa Harry Kane, an fara nuna damuwa kan rashin karsashi daga dan wasan gaba na Masar da ke taka leda a Liverpool Mohamed Sallah, wanda kawo yanzu bai taka rawar gani a kungiyarsa a kakar wasannin bana ba. Duk da cewa mai horas da kungiyar Arne Slot ya kare dan wasan tare da cewa wanann lamarin ba wani abun damuwa ba ne, amma tsoffin 'yan wasa da masu sharhi kan harkokin kwallon kafa na danganta wannan koma baya da Sallah ya samu da rashin ba da kai, baya ga zuwan sabbin 'yan wasa da kuma canja salon taka leda da kungiyar ta yi, kuma an sa ran dan wasan mai shekaru 33 zai sake farfado da ruhinsa a nan gaba. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani