Shirin Labarin Wasanni
June 7, 2021Kungiyar kwallon kafar Jamus ta 'yan kasa da shekaru 21 da haihuwa ta lashe kofin wannan rukuni na kasashen Turai, bayan da ta yi nasarar doke takwarta ta Portugal da ci daya mai ban haushi a wannan Lahadi, a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan a fara babbar gasar neman lashe kofin kasashen Turai. Godiya ta tabbata Lukas Nmecha da ke da tushe da Najeriya wanda ya cire wa Jamus kitse a wuta. Hasali ma, gwarzon ya godewa abokan wasansa da mai horaswa Stefan Kuntz yana mai cewa "Dole ne in gode wa Ridle Baku saboda taimakon da ya yi na ba ni kwallon da na ci, kamar yadda ya yi a wasa da muka yi da Netherlands. Dukan 'yan wasan sun nuna kwazo sosai. Har yanzu ba yarda cewa mun lashe wannan gasa ba. Muna godiya ga koci Stefan Kuntz, wanda ke ba mu horo mafi kyau. Muna son mu burge shi. Baya ga kasasncewar mu kungiya, mu tawaga ce ta abokan juna, kuma muna son nuna bajinta ko wani lokaci. Muna magana da yawa game da darajar gasa, amma abin da ke da muhimmanci shi ne mun ci nasara." Wannan shi ne karo na uku da Jamus kofin turai na 'yan kasa da shekaru 21 a tarihinta, bayan 2009 da 2017.
An dage bikin fitar da jadawalin CAF
Annobar corona ta sa Hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka CAF ta dage bikin fitar da jadawalin gasar cin kofin wannan nahiya da ya kamata ya gudana a Yaounde babban birnin Kamaru a ranar 25 ga watan Yuni mai zuwa. Cikin sanarwa da ta fitar, CAF ta ce rashin tabbas a dangane da hanyoyin hana yaduwar COVID-19 ne ummal aba'isan daukar wannan mataki. Ko da shi ke Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta ce nan gaba kadan za ta sanar da ranar da za a yi bikin hada kasashen, amma wannan ba shi ne karon karfo ga gasar da kamaru za ta dauki bakunci ke cin karo da kalubale ba. Idan za a iya tunawa, a bara ya kamata a gudanar da gasar ta AFCON, amma annobar corona da ta zama ruwan dare ta sa aka kai gasar zuwa shekara ta 2021. Sannan kuma CAF ta dakatar da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da ya kamata a fara a cikin wannan wata na Yuni zuwa watan Satumba don gudun yada cutar corona.
Wasannin share fage a gabanin kofin duniya
Kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Afirka na ci gaba da gudanar da wasannin sada zumunci da nufin daura damarar tinkrara wasannin share fagen shiga kofin duniya da Qatar za ta dauki bakunci. A daren Lahadi zuwa wannan Litinin Mali ta sha kashi a hannun Algeria mai rike da kambun zakarun Afirka, kuma Riyad Mahrez ne ya ci wa Fennecs ta Aljeriya daya-dayan kwallon. A wannan Litini ne Togo ke fuskantar Mene ta Jamhuriyar Nijar, yayin da Ruwanda ke karwa da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ita kuwa Sper Eagles ta tarayyar Najeriya za ta yi zagaye na biyu na wannan wasa a kasar Austria a gobe Talata, bayan kashi da ta diba a wasanta da Kamaru ci nema da daya. Wannan dai ba ya rasa ansaba da dimbim matsaloli da suka kunno kai daga sassa daban-daban ciki har da rashin biyan yan wasa da mai horas albashinsu na tsawon watanni, lamarin da ya sa wasu 'yan wasan Najeriya kin shiga a dama da su a wasanni sada zumunta. Anya a irin wannan hali, kwalliya za ta biya kudin sabulu kuwa? ma'ana 'yan tawagar super eagles za su sami kuzarin taka rawar gani kuwa? Wakilinmu a Bauchi Aliyu Muhammad Waziri ya ji ta bakin masharhanta da ma'abota kwallo a Bauchi, da rahoton da ya aiko mana.
Abdoul Razak Alfaga gwarzon Afirka
Shahararren dan damben Taekwondo na kasar Nijar Abdoul Razak Issoufou da aka fi sani da lakabin Alfaga, ya zamo zakaran Afirka na ajin masu matsakaicin nauyi na ‘yan kasa da kilo 87 na shekara ta 2021. Wannan gasar wacce ta gudana daga ranar biyar zuwa shida ga wannan wata na Yuni a Dakar babban birnin kasar Sénégal, ta hada ‘yan wasa 864 da suka fito daga kasashen Afirka 54. Da ma dai Alfaga shi ne zakaran duniya na masu wannan ajin nauyi, lamarin da bai ba da mamaki wajen lashe abjintar taekwondo ta Afirka ba. Sannan baya ga Alfaga wata ‘yar Nijar din mai suna Takiath Ben Yousouf ta zamo zakaran Afirka ta masu nauyin kasa da kilo 57. Tuni da ma dai wadannan ‘yan wasa biyu na kasar Nijar Ben Youssouf da Alfaga suka samu tikitin cancantar shiga wasannin Olympic na watan Yuli a kasar Japan. A fagen Tennis, mako guda bayan da fitacciyar 'yan wasa Naomi Osaka ta ya da kwallo domin ta rabu da kuda a gasar Roland Garros, Shi ma Roger Federer ya fice daga gasar bisa dalilai na kiwon lafiya. Dama dai bai gama murmurewa daga tiyatar gwiwa da aka yi masa ba, lokacin da Federer ya shiga gasar Wimbledon a watan Maris. Amma kuma shi dan wasan na Tennis na kasar Switzerland da ya lashe kofin Grand Slam 20, ya lashe wasan zagaye na uku da Dominik Köpfer na Jamus kafin ya janye daga zagayensa da zai yi da Matteo Berrettini na Italiya. Ita kuwa Serena Williams tsohuwar lamba daya ta duniya, an yi waje road da ita a jiya Lahadi a zagayen neman zuwa quater final, bayan da 'yar Kazakstan Elena Rybakina ta doke ta. A nasa bangaren, mai matsayi na biyar da duniya a bangaren maza Stefanos Tsitsipas ya doke dan Spain din Pablo Carreno (6-3, 6-2, 7-5), lamarin da ya ba shi damar cancanta zuwa wasan kusa da na karshe na Roland-Garros.