1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Labarin Wasanni: 08.01.24

Mouhamadou Awal Balarabe AH
January 8, 2024

Côte d Ivoire da Mali sun yi abin yabo yayin da Kwango da Mozambik suka yi abin fallasa a sharar fagen gasar cin kofin kwallon kafar Afirka da za a soma nan gaba kadan a Cote d'Ivoire.

Hoto: Muzi Ntombela/BackpagePix/empics/picture alliance

A yayin da rage kwanaki biyar a fara gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika a kasar Côte d Ivoire, kungiyoyin kasashen da abin ya shafa na ci gaba daura damara inda suka gudanar da wasannin sada zumunta wadanda sakamakon suka bambanta daga wannan tawaga i zuwa wancan. Côte d' Ivoire da ke karbar bakuncin gasar ta Afcon ga misali, ta nuna cewar ba ta son a zo gidanta a fi ta iya taka rawa, inda ta yi wa Saliyo dukan kawo wuka ci 5-1 a wasan da ta yi a birnin San Pedro. 'Yan wasan biyar daban-daban ne suka zura kwallayen tare da ba wa Côte d' Ivoire damar yin nasara, lamarin da ke nuna hadin kan tawagar da kuma yawan askarawanta na gaba da za su iya cire mata kitse a wuta. Ko da Jean-Louis Gasset da ke horas da tawagar ta Côte d' Ivoire sai da ya nuna gamsuwa da kamun ludayin 'yan wasansa.

"Wasa ne da ya kawo karshen horon da muka yi wanda komai ya wuce da kyau. Muna son mu kasance cikin yanayin gasar Afcon ko CAN, mun so mu sha wahala, mu kara kaimi don ganin yadda kungiyar za ta saje, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu."Ita kuwa Guinea Bissau ta dibi kashinta a hannun Mali da ci 6-2 a Bamako, alhali a lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci, da ci 3-2 ga Aigles ta Mali ke casa Guinea, ko da shi ke sakaci ya sa 'yan mali dada mamaye su. Amma dai kocin Mali Eric Chelle ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba a kungiyarsa yayin da gasar ke gabatowa.

Hoto: Gabriel Ahiabor/Shengolpixs/imago images

" A jimlance dai, nasara ce da ke kunshe da adadi mai yawa na kwallaye a raga da ingancin wasa wanda ya zarta wa sa'a. Amma kuma a daya hannun, akwai manyan kura-kurai da suke tafkawa wadanda suke haifar da illa. Akwai aiki da ya kamata a gudanar dangane da maida hankali. Kada a tuna cewa an gama komai, an yi nasara." A sauran wasannin share fage da suka gudana a karshen mako kuwa, Tunisiya da Moritaniya sun tashi 0-0, yayin da Masar ta samu nasara a kan Tanzania da ci 2-0. Abin mamakin ma shi ne yadda Mohamed Salah ya baras da bugun fanareti a yayin wannan wasa. Ita kuwa Mozambik cikin sauki ta lallasa Lesotho da ci 2-0. A nata bangaren, Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango ta fada tarkon Angola inda suka tashi 0-0.

Hoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa Super Eagles ta Najeriya tana ci gaba da barje gumi a wasannin sada da zumunta  da Burkina Faso da kuma tsibirin Cap Verde a daidai lokacin da gasar ta Afcon ke dada karatowa. Duk da hasashen da ake cewar Najeriyar za ta iya taka rawar gani domin tana da zakakuran 'yan wasanta irin Victor Osimhen da Boniface da ke bugawa a Leverkusen ta Jamus, amma dai rashin kishi na iya kawo mata tarnaki. A ranar Asabar za a gudanar da bikin bude gasar ta Afcon tare da gudanar da wasan farko tsakanin Côte d' Ivoire mai masaukin baki da Guinea Bissau .

Hoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/Imago Images

A nan Turai kuwa, a daidai lokacin da gasar Bundesliga ta Jamus ke ci gaba da hutun shiga sabuwar shekara har i zuwa karshen mako, sauran manyan Lig sun koma fagen wasa musamman Seria A na Italiya da ke daf da kammala zagayen farko. Tuni ma Inter Milan ta lashe kwarya-kwaryar kambun zakara na rabin wa'adi bayan nasarar da ta samu a kan Hellas Verone da ci 2-1. Juventus ce ke biya mata da yawan makai bayan da  ta doke Saler-nitana da ci 2-1. Sannan AC Milan da a nata bangare ta doke Empoli da ci 3-0 ta na a matsayi na uku na teburin Serie A. A Ingila kuwa, fagen ya koma ga wasannin kalubale na neman cin kofin kwallon kafar kasar da aka fi sani da kofin FA, wanda aka gudanar da zagaye na 3. Kuma wasan da fi daukar hankali shi ne fafata da aka yi tsakanin Arsenal da Liverpool, inda Reds ta yi nasaar da ci 2-0, duk da cewa shakarurin dan wasanta Mohamed Salah bai taka leda ba saboda yana halatar gasar Afcon. A sauran wsannin kuwa, wasu kungiyoyi da ake damawa da su a gasar Premier ba su ji dadi ba saboda an doke su, irin su Luton Town da Nottingham Forest da kuma West Ham.

Hoto: Stefan Brauer/DeFodi Images/picture alliance

A kasar Faransa ma, an kai matakin da wasu kungiyoyin da ke bugawa a Ligue 1 suka shiga a dama da su a yunkurin neman lashe kofin kwallon kafar kasar karo na 32. Sai dai tuni aka yi wajen road da wasu daga cikinsu kamar Lorient da Sochaux ta doke ta. Ita ma Metz ta ga arkana domin 'yar baya ga dangi na babban lig Clermont ce ta cire ta, yayin da Lens ta yi rashin nasara a hannun Monaco. Duk sauran manyan kungiyoyin za su buga wasan zagaye na gaba ciki har da Paris Saint-Germain, wadda ta yi nasara da ci 9-0 a kan kungiyar US Revel da ke bugawa a lig na shida. A karshe a kasar Spain ma dai, an buga wasanni kalubale ne neman lashe Copa del Rey karo na 32 kuma babu wani kare bin damo domin duk manyan kungiyoyi sun samu damar zuwa zagaye na gaba, wadanda suka hada da Real Madrid da FC Barcelona da kuma Atletico Madrid.

Hoto: Yazeed Aldhawaihi/AP/picture alliance

Yanzu kuma sai mu shiga fagen dambe, inda shahararren dan boxing dan asalin Kamaru Francis Ngannou ya san abokin hamayyarsa na gaba, wanda ba wani ba ne illa Anthony Joshua na Burtaniya. Wannan jadawalin ya ja hankali ne saboda Ngannou da ke zama tsohon tauraron MMA ya taka rawar gani a damben farko da ya yi da Tyson Fury da ke zama daya daga cikin mafi shahara a duniya. Ko da shi ma Anthony Joshua ba kanwar lasa ba ne, domin ya taba zama zakaran Olympic na boxing a 2012, sannan ya taba zama zakaran duniya na azuzuwan IBF da WBO da WBA a tsakanin 2016 zuwa 2021. Tuni ma dai dan Kamaru ya yi amfani da kafofin sada zumunta wajen yi wa magoya bayansa alkawarin ba da mamaki a shekarar 2024, a daidai lokacin da ya rage watanni a yi karon battan tsakanin Ngannou da Joshua a birnin Ryad na Saudiyya.

Hoto: Dylan Martinez/Reuters

Al'amura sun dagule wa gwanin dan wasan tennis Rafael Nadal jim kadan bayan dawowarsa fage, inda ya janye daga gasar Australian Open wanda za a fara a cikin mako guda. Shi tsohon lamba daya a duniya, wanda aka gamu da tsagewar kwanji, baya son yin kasadar jefa rayuwarsa cikin hadari, bayan da dama ya shafe kwanaki 347 ba tare da wasa ba saboda rauni a kugu. Sai dai har yanzu Rafael Nadal na kan bakarsa na shiga gasar Roland Garros a watan Mayu mai zuwa domin ya yi kokarin lashe kambu na 15 a Faransa.