1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shirin Labarin Wasanni

Suleiman Babayo RGB
March 8, 2021

Sakamakon wasannin lig na Jamus da batun birnin da zai dauki bakuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle a shekarar 2032. Annobar corona ta sa al'ummar Japan zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na karbar bakuncin gasar.

Bayern München - Borussia Dortmund
Hoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

Sakamakon wasannin lig na Jamus da batun birnin da zai dauki bakuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle a shekarar 2032. Annobar corona ta sa al'ummar Japan zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na karbar bakuncin gasar mai zuwa. A wasannin lig na Jamus da ake kira Bundesliga da aka kara a karshen mako sakamakon ya nuna, Schalke da Mainz ba kare bin damo, Leverkusen ta ci Monchengladbach kwallo guda a yayin da Hoffenheim 2-1 Wolfsburg, Bayern 4-2 Dortmund.

Fifa na zargin Ahmad Ahmad da aikata ba daidai baHoto: picture-alliance/dpa/Str

Ranar Juma'a mai zuwa 12 ga wannan wata na Maris a birnin Rabat na kasar Moroko ake zaben shugabancin hukumar kula da wasannin kwallon kafa na nahiyar Afirka, inda Shugaban hukumar Ahmad Ahmad dan kasar Madagaska ke neman wa'adi na biyu inda zai fafata da 'yan takara da suka hada da shahararren mai arziki Patrice Motsepe dan kasar Afirka ta Kudu. A wannan Litinin  Ahmad Ahmad zai san matsayinsa bisa daukaka kara kan dakatar da shi da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasashen duniya, FIFA ta yi na tsawon shekara biyar saboda zargin saba ka'ida. Akwai wasu kasashe da ba su nuna adawa da takarar shugaban hukumar a karo na biyu ba duk da wannan zargi da yake fuskanta.

Kwamitin Olympics na nazarin kasar da za a gudanar da gasar 2023Hoto: AP

Kungiyar shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics, IOC, ta ce ta fi so birnin Brisbane da ke jihar Queensland a Australiya ya dauki nauyin gasar wasannin a shekara ta 2032, wato tsakanin nan da shekaru goma sha daya masu zuwa. Amma duk da nuna amincewarta da birnin, dole sai kungiyar ta kada kuri’ar da za ta tabbatar da hakan. Idan kuri’ar ya je yadda ake zato, wannan zai zama karo na uku da kasar Australiya za ta dauki nauyin gasar wasannin Olympics.