Labarin Wasanni 10.08.2026
August 10, 2026
Za mu yaye kallabin shirin ne da fagen kwallon kafa, inda tafiya ta yi nesa a kokarin da kasashe ke yi na lashe gasar cin kofin Afirka ta mata da ke gudana a kasar Maroko. Hasali ma a matakin kusa da kusa da na karshe da ya gudana a karshen mako, an samu sakamakon da ba a zata ba musamman ma a karawa da aka yi tsakanin giwar kwallon matan Afirka Super Falcons ta Najeriya da Indomitables lionesses ta Kamaru.
Sabanin hasashen da aka yi tun da farko, 'yan matan kamaru ne suka karya lagon 'yan matan Najeriya da ke rike da kambun kwallon kafar nahiyar Afirka, inda suka doke su da ci 1-0. Godiya ta tabbata ga Myriam Nyadjou da ta zura kwallon a raga minti na 20 bayan fara wasa, kuma duk kokarin da 'yan Super Falcons suka yi don farke kwallon da ake bin su ya je ga uwa banza.
Duk da cewa sau 10 cikin tarihi Super Falcons na lashe kofin kwallon mata na Afirka, amma cire su da aka yi kafin su tafi matakin kusa da na karshe, bai yi wa 'yan kasar dadi ba. Kuma wannan rashin nasarar ta sa Super Falcons rasa tikitin shiga gasar cin kofin mata ta duniya da kasar Brazil za ta karbi bakunci a shekarar 2027, har sai ta shiga matakin tankade da rairaya.
'Yan matan na kamaru za su fafata ne da Maroko mai masaukin baki a wasan kusa da na karshe, sakamakon doke Afirka ta Kudu da ci 2-1.
A sauran wasannin kwata fainal da suka gudana kuwa, Malawi da wannan shi ne karon farko da ta shiga gasar kwallon matan Afirka ta shammaci Ghana da ci 2-1. Saboda haka ne ita Malawi za ta fafata da Aljeriya a wasan kusa da na karshe bayan da ta tuntsurar da 'yan matan Côte d' Ivoire da 2-1.
Za a buga wasan kusa da na karshe a ranar Laraba kuma an shirya gudanar da wasan karshe na Wafcon a ranar Alhamis 13 ga Agusta. Sannan ta tabbata cewar duk kasashe da suka kai matakin kusa da na karshe na kwallon matan Afirka sun samu tikitin shiga gasar kwallon kafa ta duniya, wadanda suka hada da Kamaru da Malawai da Aljeriy da Maroko.
A daidai lokacin da manyan lig na kasashen Turai ke shirin tinkarar sabuwar kakar wasannin, cinikin 'yan kwallo na ci gaba da kankama, inda manyan kungiyoyi biyu Roma da Aston Villa suke kai goro da mari don ganin cewa Real madrid ta ba su araon dan wasanta na gaba Endrick, mai shekara 22. Sai dai jaridun da ke maida hankali kan harkokin wasannin sun ruwaito cewar zakakurin dan wasan Bayern Munick kuma kyaftin na babbar kungiyar Ingila Harry Kane, na shirin tsawaita kwantiraginsa da zakaran kwallon Jamus har zuwa shekarar 2029. A nata bangaren Barcelona da ke rike da kamnun zakaran Sifaniya na ci gaba da naci wajen cefano Rodri, mai shekara 30, inda ta yaukaka tayin da ta yi wa Manchester City.
Yanzu kuma sai mu tsunduma babin rikicin da ke faruwa a FIFA, inda Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta yi Allah wadai da abin da ta danganta da "kawancen da wasu ke yi da niyyar hambarar da Gianni Infantino daga shugabanci, tare da neman raunana FIFA. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, hukumar ta nuna goyon bayanta da Gianni Infantino, inda ta ce "rahotanni da aka buga a jaridu ba su tantance tare da tabbatar da zarge-zarge maras tushe da suka shafi FIFA da shugabanta ba," Amma FIFA ba ta bayyana wadanne zarge-zarge ba.
A cewar wani labarin da aka buga a jaridar Birtaniya "The Telegraph" a daren Juma'a, Gianni Infantino na fuskantar suka mai karfi tun bayan janye shirinsa na bude hannun jari ga 'yan kasuwa a karshen watan Yuli. Sannan Shugaba Infantino na fuskantar zargin nuna fifiko a lokacin da yake aiki a hukumar kwallon Turai UEFA.
A cewar jaridar ta Birtaniya, tsohon babban sakataren UEFA tsakanin 2009 zuwa 2016, ya yi amfani da mukaminsa wajen daukaka wata ma'aikaciyar hukumar da yake da alaka ta kud da kud da ita. Telegraph da ba ta ambaci majiyoyinta ba, ta ce wannan ma'aikaciya ta samu "kunshin kudin sallama mai tsoka" daga UEFA, bisa amincewar Infantino. Sannan shekara guda bayan haka, an biya mata kudin makaranta kusan 50,000 Euro a lokacin da ta je kara ilimi. Sai dai FIFA ta musanta wadannan zarge-zargen.
Sannan, da ya sake tsayawa takarar shugabancin FIFA a zaben watan Maris mai zuwa, yana shan suka game da shugabancinsa, musamman daga hukumomin Turai na arewacin Amurka UEFA da CONCACAF. A fannin jagororin kasashe ma dai an fara juya wa Infantino baya, inda firayim ministan Kanada Mark Carney ya nuna rashin "kwarin gwiwa" ga Gianni Infantino. Hasali ma dai, Kalubalen da shugaban FIFA ke fuskanta na karuwa kowace rana, inda hukumar kwallon kafa ta Norway ke neman Gianni Infantino ya yi murabus a hukumance, kamar yadda shugabanta Lise Klavness ta bayyana.
Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF ba ta gamsu da zarge-zargen da ake wa Infantino ba, inda maimakon haka ta jaddada goyon bayanta ga Gianni Infantino a zabe mai zuwa.
A fagen tennis, 'yar Kazakhstan Elena Rybakina, da ke da matsayi na biyu a duniya a rukunin mata, da Coco Gauff 'yar Amurka mai matsayi na hudu, da kuma tsohuwar labba daya ta duniya Naomi Osaka sun cancanci shiga zagayen kwata-kwata na gasar WTA 1000 a Toronto. Sai dai tun ranar Asabar, ana fitar da Aryna Sabalenka, lamba daya ta duniya da Jessica Pegula (lamba 3), wacce lashe gasar ta Kanada a 2023 da 2024.