1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
February 15, 2021

Dan damben boxing na Najeriya Kamaru Usman ya kafa tarihi, bayan da ya yi wasa 13 na duniya a jere ba tare da samun koma baya ko da sau guda ba.

UFC I Kamaru Usman I  Mixed martial artist
Hoto: Diego Ribas/PX Imagens/ZUMA/picture alliance / ZUMAPRESS.com

Zakaran damben boxing na duniya ajin masu matsakaicin nauyi Kamaru Usman na Najeriya, ya sake samun nasara a karo na 13 a jere ranar Asabar a birnin Las Vegas na Amirka a kan abokin hamayyarsa Gilbert Burns dan kasar Brazil. Shi dai wannan dan damben da ake wa lakabi da "Mafarki mai ban tsoro" dan Najeriya, ya fara da shan duka a turmi na farko kafin daga bisani ya ramawa kura aniyarta a turmi na biyu, sannan ya yi wa Gilbert Burns mugun kisa, wanda ya sanya alkalin wasan dakatar da damben. Wannan nasarar ta Kamaru Usman ta ba shi damar kafa tarihin yawan nasarori a rukuninsa. Gwarzon dan wasan, ya sha gaban shahararren dan damben Kanada Georges St-Pierre kuma ya shiga cikin jerin taurarin MMA (Mixed Martial Arts). Tuni ma Kamaru Usman ya ce a shirye yake ya dauki fansa a kan dan damben Amirkan nan Jorge Masdiva wanda ya kayar da shi a watan Yulin da ya gabata.

Mako guda bayan kammala gasar kwallon kafa ta 'yan wasan Afirka da ke bugawa a kasashensu na asali, Moritaniya ta karbi bakuncin gasar wannan nahiya ta 'yan kasa da shekaru 20 da haihuwa, wacce za a shafe makonni uku ana gudanarwa. Kuma kamar yadda aka saba, bayan kasaitaccen bikin bude gasar a Nouakchott babban birnin kasar, Moritaniya mai masaukin baki ba ta ji dadi a hannun Indomitable Lions a wasan farko ba, inda Kamaru ta doke ta da ci daya mai ban haushi a ranar Lahadi, lamarin da ya sa Kamaru jin kamshin mataki na gaba ba.
Wannan dai shi ne karon farko da Hukumar Kwallon Kafa ta Kasashen Afirka CAF ta fadada gasar 'yan kasa da shekaru 20 da haihuwa, zuwa kasashe 12 maimakon takwas kamar yadda aka saba a baya. Sannan wannan shi ne karon farko da Moritaniya ke halartar gasar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 20 da haihuwa a Afirka. Sai dai a wannan karon kasashen Mali da Zambiya da suka fi taka rawar gani, ba su cancanci shiga gasar ba. Wasanni uku ne za su gudana a wannan Litinin ciki har da karawa da za a yi tsakanin Namibia da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ita kuwa kungiyar matasan Moritaniya za ta yi wasanta na biyu a ranar Laraba da Mozambik, wacce ita ma ke zama sabon shiga. Yayin da Kamaru da ke saman teburi da maki uku a rukunin A za ta kara da Yuganda.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kamaru Indomitable Lions Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

Har yanzu dai muna a nahiyar Afirka, inda a karshen mako aka fara gudanar da matakin rukuni na neman cin kofin gasar zakarun kwallon kafa na wannan nahiya wato Champions League. Abin da ya fi daukar hankali shi ne rashin kwazo na kungiyoyin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango guda biyu, inda TP Mazembe da ke fada ana ji a Afirka ta kasa tabuka komai a gaban Belouizdad ta Aljeriya, inda aka tashi wasan canjaras babu ci, yayin da a wasan da ta yi a gida AS Vita Club ta debi kashinta a hannun SImba SC ta Tanzaniya da ci daya da nema. Sai dai Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta yi nasarar lallasa Al Hilal ta Sudan da biyu da nema. Wani abin yabo shi ne yadda dan hakin da aka raina Horaya AC zakaran Guinea Conokry ta doke Petro Atletico ta Angola da ci biyu da nema. Ita kuwa Esperance ta Tunusiya ta samu nasara a kan sabon shiga Teungueth ta Senegal da ci biyu da daya, yayin da Zamalek da MC Alger suka tashi ba wanda ya ci wani.
Yanzu kuma sai mu tsallako gida Jamus, inda kwanaki kalilan bayan lashe bajintar zakaran zakarun kulob na duniya, Bayern Munich ta sayi daya daga cikin 'yan wasan RB Leipzig, wanda ba wani ba ne illa dan wasan baya dan kasar Faransa Dayot Upamecano wanda zai koma Munich a kakar wasa mai zuwa. Wannan sauyin kulob ya zo ne a lokacin da  RB Leipzig ta sami nasara ci biyu da daya a kan Augsburg a mako na 21 na Bundesliga. Wannan ya sa ta ci gaba da rike matsayinta na biyu a tebrin Bundesliga da maki 44, yayin da Bayern da ke bisa terbur za ta yi wasanta da Armenia Bielefeld a yammacin wannan Litinin. 

Dayot Upamecano dan wasan baya na kungiyar RB Leipzig ta JamusHoto: picture-alliance/AP Images/J. Meyer

Sai dai Borussia Dortmund ta kasa yin abin yabo a filin kwallonta na Signal Iduna Park, a karawar da ta yi a mako na 21 na Bundesliga da takwarta da Hoffenheim duk da baras da kwallaye da bakuwartata ta yi, inda aka tashi wasan ci biyu da biyu. Wannan sakamakon ya sa har yanzu BVB na matsayi na shida da maki 33, lamarin da ya dada dakushe fatanta na shiga rukunin kungiyoyin da za su wakilci Jamus a gasar zakarun Turai na Champions League ko kofin Turai na Europa League. Ko da dan wasanta na tsakiya Marco Reus sai da ya bayyana takaicinsa dangane da mummunan sakamako da suka samu.

Tafiya ta fara nisa a muhimmiyar gasar Tennis da ke gudana a birnin melbourne na kasar Ostireliya, inda bayan wasanni tankade da rairaya a kan san 'yan wasa da suka haye matakin kusa da kusa da na karshe wato qzater final. A rukunonin maza, Rafael Nadal ya kai wasan daf da na karshe a gasar Australian Open bayan nasarar da ya samu a ranar Litinin. A rukunin mata kuwa Serena Williams da Simona Halep ne za su kara a wasan kusa da na karshe na Australian Open, za a buga da yammacin Talata a kotun Rod Laver. Ita ma lamba dayan tennis ta duniya Ashleigh Barty, yar Ostireliya ta tsallake zuwa zagayen kwata fainal na gasar ta Australian Open ta hanyar yin fatali da  Amirka Shelby Rogers. Wannan wasa na kwallon Tenis na daya daga cikin wasannin da aka dade ana yinsu a Tarayyar Najeriya tun zamanin Turawan mulkin mallaka, abin da ya sanya 'yan wasan tennis kan wakilci Najeriya a kasashen waje a wasu lokuta.