Shirin Labarin Wasanni
May 17, 2021Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Bayern Munich ta Jamus Robert Lewandowski ya shiga cikin kundin tarihi, inda ya kasance dan wasan Bundesliga na biyu da ya yi nasarar zura kwallaye 40 a kaka guda. Hasali ma bugun fanareti a wasa da Freiburg a ranar Asabar da yamma ne, ya sa wannan dodon raga dan kasar Poland ya kama kafafun Gerd Müller wanda ya zira adadin wadannan kwallaye shekaru 49 da suka gabata. Abin lura a nan shi ne, dukkanin gwanayen 'yan wasan wato Müller da Lewandowski suna bugawa a Bayern a lokacin da likkafar tasu ta ci-gaba. Robert Lewandowski ya yi ma amfani da wannan dama wajen jinjina wa mutumin da ya gada, ta hanyar bayyana rubutun da ya yi a cikin rigarsa ta ciki jim kadan bayan cin kwallonsa, inda ya rubuta "4-ever Gerd".
Wannan ba ya rasa nasaba da cutar Alzeimer da Gerd Müller ke fama da ita, shekaru 51 bayan lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar 1970. Shi dai Lewandowski yana da damar inganta wannan bajintar yawan kwallaye, domin kungiyarsa ta Bayern Munich za ta kara da Augsburg a makon karshe a Allianz Arena. VfL Wolfsburg da Borussia Dortmund suka samu tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai, saboda abin mamakin da Eintracht Frankfurt ta yi na shan duka a hannun Schalke 04 da ta koma karamin lig da ci uku da hudu. Saboda haka Frankfurt za ta buga gasar Europa Lig a kaka mai zuwa. Wannan cancantar ta Dortmund bayan da ta doke Mainz uku da daya a makon kusa da na karshe na Bundesliga, ya ba ta damar cika burin da ta sa a gaba baya ga lashe kofin kalubalen Jamus da ta yi a makon da ya gabata.
Hakan dai ya faranta ran mai horas da 'yan wasan kungiyar ta Dormund na rikon kwarya da kwantiragensa ke kare wa, Edin Terzic: "Muna matukar farin ciki. Mun fara samun jerin nasarori a wasannin a lokacin da ya dace a kakar wasa. Mutane kalilan ne suka yi imani da zubin da muka yi, bayan rashin sa a a wasa da Frankfurt a farkon watan Afrilu. Duk da haka muka ci gaba da gwagwarmaya, don fita daga wannan matsalar na rashin kyan sakamako. Sannu a hankali muka rage tazara tare da abokan karawarmu, inda a karshe muka cancanci shiga gasar zakarun Turai kwana daya kafin karshen kakar wasannin. Labari ne mai ban mamaki."
Wasannin na ranar Asabar sun bai wa kungiyoyi uku damar ci gaba da kasance a babban lig din kwallon kafar Jamus. Hasali ma doke Bremen da ta yi da biyu da nema, ya bai wa Augsburg damar ci gaba da damawa a Bundesliga, har ma ta tabbatar wa Hertha Berlin gurbinta duk da canjaras babu ci da ta yi da Cologne. Ita ma Mainz ta tsira daga halin gangarawa duk da lallasata da Borussia Dortmund ta yi. A wasannin mako mai zuwa da ke zama na karshen kaka dai, kungiyoyi uku za su yi kokarin fidda kansu daga fadawa karamin lig wato Arminia Bielefeld da Werder Bremen da kuma FC Cologne.
A nahiyar Afirka, an gudanar da zagayen farko na wasan kusa da kusa da na karshe wato quater final na neman cin kofin Confederation a karshen mako, kuma kungiyar Pyramids FC ta Masar wacce ta buga wasan karshe a bara, ta yiwa Enyimba ta Najeriya dukan kawo wuka da ci hudu da daya a birnin Alkahira. Ita kuwa CS Sfaxien ta Tunisiya da ke zama kungiya mafi nasara a gasar ta yi abin fallasa a gida, inda JS Kabylie ta lallasa ta da ci daya mai ban haushi. Yayin da Coton Sport ta Garoua Kamaru ta yi nasara a kan ASC Jaraaf ta kasar Senegal da ci daya mai ban haushi. Su kuwa Orlando Pirates ta Afirka ta Kudu da Raja Casablanca ta Maroko, sun tashi wasa kunnen doki daya da daya. Za a gudanar da zagaye na biyu na kwata final na Confederation Cup din, a ranar Lahadi 23 ga wannan wata na Mayu.
Tawagar da Hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka ta aika Kamaru don shaidar da inda aka kwana a shirye-shiryen daukar bakunci gasar nahiyar a badi, ta kammala aikinta. Duk da yaba inda aka ware da kuma kawata inda za a gudanar da bikin hada kasashe zuwa rukuni-rukuni, amma kuma tawagar ta CAF ta nuna rashin gamsuwa da jan kafa da hukumomin kamaru ke yi wajen kammala ginin filin wasa na Yaounde. Saboda haka ne ma ta dibarwa kasar wa'adin watanni biyar domin ta kammala gina sabon filin wasan ko kuma CAF ta dauki matakin da ya dace. Kwamitin zartarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasashen Afirkan CAF ya yi zamansa a karshen mako a birnin Kigali na kasar Ruwanda, inda ya yanke shawarar dage wasannin wannan nahiya na share fagen shiga gasar neman cin kofin Duniya da za ta gudana a Qatar a shekara ta 2022.
A maimakon gudanar da su a wata mai kamawa na Yunin 2021 dai, sabon jadawalin da aka tsayar ya tanadi gudanar da wasannin neman cancantar a watannin Oktoba da Nuwamban 2021 da kuma watan Maris na 2022. Sannan kuma kwamitin na CAF ya amince da kasashen da za su dauki bakuncin manyan gasannin da ke tafe a nahiyar Afirka. A yanzu dai an tsayar da Masar a matsayin inda za a buga wasan karshe a watan Nuwamba na kofin zakarun Afirka na kakar 2020-2021. Yayin da wasan karshe na badi na Champions League aka tsara gudanar da shi a ranar 17 ga Yulin 2021 a kasar Moroko. A Bangaren gasar Confederation Cup kuwa, wasan karshe na bana, za a buga shi a Jamhuriyar Benin a ranar 10 ga Yulin 2021.