1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Suleiman Babayo LMJ
October 19, 2020

Shirin na dauke da sakamakon wasannin lig-lig da aka gudanar a karshen mako a kasashen Turai gami da sake farfadowar harkokin wasanni a Ghana bayan annobar cutar coronavirus.

Deutschland Bundesliga 1. FC Köln gegen Eintracht Frankfurt
Fafatawa tsakanin FC Cologne da Eintracht Frankfurt Hoto: Mika Volkmann/Getty Images

A wasan lig-lig na Jamus da ake kira Bundesliga na karshen mako, babu wata kungiya da ta kara wasa a gida ta samu nasara sai dai kunnen doki ko kuma ta sha kaye. Hoffenheim ta sha kashi a gida a hannun Dortmund da ci daya da nema Freiburg ta yi kunne doki daya da yada tsakaninta da Bremen yayin da Stuttgart ta bi Hertha Berlin har gida ta kuma lallasa ta da ci biyu da nema. 

Mainz ma ba ta ji da dadi ba a hannun Leverkusen, domin kuwa an bi ta har gida an kuma lallasa ta da ci daya da nema. Bayern ta  bi Arminia har gida kuma ta yi mata cin kaca da hudu da daya. Sannan Augsburg da RB Leipzig ma an tashi wasa ne biyu da nema a gidan Augsburg din. Kawo yanzu Leipzig ke jagorancin teburin da maki 10, sai Bayern Munich a matsayi na biyu da maki tara a matsayi na uku akwai Dortmund ita ma da maki tara yayin da kungiyar Eintracht Frankfurt ke matsayi na hudu da maki takwas.

Karawa tsakanin Chelsea da SouththamptonHoto: Matthew Childs/AFP/Getty Images

A wasannin Premier League na Ingila kuwa, Everton ta yi biyu da biyu tsakaninta da Liverpool, haka abin yake tsakanin Chelsea da Southampton inda suka tashi uku da uku yayin da Manchester City ta samu nasara a kan Arsenal da ci daya da nema. Newcastle kuwa ta sha kashi a gida a hannun Manchester United da ci hudu da daya. A wasannin La Liga da aka fafata a Spain kuwa, kungiyar Real Madrid ta gamu da rashin nasara a hannun kunguiar Cadiz da ci daya mai ban haushi. Sannan Villarreal ta doke Valencia da ci biyu da daya kana kungiyar Atlético ta samu nasara kan Celta da ci biyu da nema.

A jerin gwanayen Tennis na duiniya da ake fitarwa a wannan karon: Novak Djokovic, dan kasar Sabiya na kan gaba a matsayin na daya da maki dubu 11 da 740 Rafael Nadal dan kasar Spain, na biye masa da maki 9,850 kana Dominic Thiem dan kasar Oustria na matsayi na uku da maki 9,125. Kasashen Jamus da Holland gami da Belgium za su nemi damar daukar gasar neman cin kofin kwallon kafa na mata na duniya na shekara ta 2027 na hadin gwiwa, kamar yadda hukumar kula da wasan kwallon kafar Jamus ta tabbatar. Ita dai Jamus za ta dauki nauyin gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Turai na shekara ta 2024 kuma samun sake damar daukar nauyin gasar kwallonm kafar matan ta duniya a shekara ta 2027, zai kara fito da sunan kasar a idon duniya.

Idan muka leka nahiyar Afirka, a kasar Ghana kamar sauran kasashen duniya, harkokin wasanni na ci gaba sake dawowa sannu a hankali bayan dakatarwa sakamakon annobar cutar coronavirus da ta addabi galibin kasashen duniya.