1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: 20.06.2022

Suleiman Babayo MAB
June 20, 2022

Yanzu haka ta tabbata cewa Sadio Mané dan kasar Senegal da ke wasa a kungiyar Liverpool ta Ingila zai koma kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus a kakar wasannin 2022-2023.

Sadio Mane
Sadio Mané zai koma Bayern MunichHoto: Anke Waelischmiller/SVEN SIMON/picture alliance

Ana gani cewa Sadio Mané zai maye shahararrren dan wasa Robert Lewandowski dan kasar Poland. Sai dai muddin Lewandowski bai samu wata kungiya ba, akwai yiwuwar Bayern Munich ta fuskanci cikas bayan dawowar dan wasa Sadio Mané. Shi dan kasar ta Senegal na daga cikin 'yan wasa da suka sa kasarsa lashe kofin kwallon na kasashen Afirka a farkon shekara ta 2022.

 

Shugaban Chelsea Bruce Buck ya taba wa Michael Ballack lambaHoto: picture-alliance/Pressefoto Ulmer

Bruce Buck zai sauka a matsayin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, kamar yadda wata sanarwa ta wannan Litinin ta tabbatar. Dan Amirkan zai sauka daga shugabancin a watan Yuni mai zuwa, amma ya ce zai ci gaba da zama a matsayin mai ba da shawara ga kungiyar. Shi dai Bruce Buck yana shugabancin tun shekara ta 2003 kuma zai sauka sakamakon sauyi saboda kungiyar ta fita daga hannun Roman Abramovich hamshakin mai arziki dan kasar Rasha.


Kungiyar kwallon kafar Austaraliya ta Socceroos ta sami damar karawa a gasar cin kofin duniya na FIFA wanda za'a fara a watan Nuwamban bana. Kungiyar ta yi wannan nasarar ne bayan da ta doke Peru a fenarti bayan da kungiyoyin kasashen biyu suka shafe miniti 120 suna fafatawa ba ci ko daya a tsakaninsu. Wannan nasara ta socceroos ta yi tasiri sosai a kasar wanda har yau ba ta taba ci kofin kwallon kada na FIFA ba.

'Yan kwallon Austaraliya sun yi atisaye a birnin Mainz na JamusHoto: AFP/Getty Images/D. Roland

 

Mykhailo Romanchuk ya nuna farin cikin samun lambar zinare a ninkayaHoto: Gregory Bull/AP/picture alliance

Mykhailo Romanchuk dan Ukraine da ya samu zinare a gasar ninkaya na duniya na mita-800 a kasar Romaniya a yayin da yaki da ke faruwa a kasarsa. Romanchuk wanda lokacin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya ya samu azurfa guda biyu ya ce wannan nasara da yake samu ya sadaukar kan fata na gari ga duniya baki daya. Sannan dan wasan na ninkaya daga Ukraine ya ce zai ci gaba samun horo domin yin nasara a gasar ninkaya da yake halarta.