Labarin Wasanni 21.10.2024
October 21, 2024A teburin wasannin Bundesligar Jamus, kungiyar Bayern Munich ce ke jagoranci da maki 17, yayin da RB Leipzig ita ma da maki 17 tana matsayi na biyu, kana Freiburg tana mataki na uku da maki 15, sannan a matsayi na hudu akwai kungiyar Bayer Leverkusen mai maki 14.
A wani labarin kuma, dan wasan Super Eagles ta Najeriya da ke Bayer Leverkusen ta Jamus, Victor Boniface ya tsallake rijiya da baya, bayan gamuwa da hadarin mota a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Frankfurt. Sanarwar da kungiyarsa ta fitar ta ce Boniface ya je filin jirgin ne don dauko wani abokinsa, inda ya samu rauni kadan, amma motarsa ta yi raga-raga, kamar yadda 'dan wasan da kansa ya wallafa hotonta a shafukan sada zumunta, kafin daga bisani ya goge. Ita dai Leverkusen ta doke Eintracht Frankfurt da ci 2-1, inda Boniface ya zura kwallo ta biyun da ta ba ta nasara.
A ranar Talata 22 ga wannan wata na Oktoba ake ra san hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF za ta bayyana hukuncin da ta yanke game da matsalar da ta faru tsakanin yan wasan Najeriya da kasar Libiya wacce har ta kai ga rashin yiwuwar wasan. Gabanin hukuncin kuma 'yan Najeriya na bayyana ra'ayinsu game da abin da suke tsammani na sakamakon hukuncin. Daga Bauchi wakilinmu Aliyu Muhammad Waziri ya duba mana wannan batu ga kuma rahoton da ya aiko mana.
Shahararren dan wasan dembe Francis Ngannou daga kasar Kamaru a ajin masu nauyi, ya doke Renan Ferreria daga kasra Brazil, tun zagayen farko, lokacin wasan da aka kara a karshen mako a kasar Saudiyya. Shi dai Ngannou ya samu wannan narasa cikin dakikoki 88. Sannan cikin hawaye bayan tashi daga wasan demben Francis Ngannou ya sakaudar da wannan nasara ga 'dan-sa Kobe wanda ya rasu a watan Afrilu na wannan shekarar yana da watanni 15 kacal da haihuwa.
A wasan tennis kuma shahararren dan wasan nan, Rafael Nadal ya yaba wa Novak Djokovic saboda taimaka masa wajen wasa fiye da yadda ya yi tunani. Shahararrun 'yan wasan biyu sun fafata a wasan kaje bujinta a karshen mako. Shi dai Rafael Nadal mai shekaru 38 da haihuwa dan kasar Sifaniya zai yi ritaya daga wasan a wata mai zuwa.