1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 23.09.2024

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
September 23, 2024

Bayern ta yi kane-kane a kan teburin Bundsliga a mako na hudu na kakar wasannin Bundesliga, yayin da Ghana ta yi rashi bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta janye wasu wasanni da aka shirya gudanar wa a kasar..

Harry Kane na daga cikin 'yan wasan Bayern da suka zura wa Bremen kwallo
Harry Kane na daga cikin 'yan wasan Bayern da suka zura wa Bremen kwalloHoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images

A yayin da aka shiga mako na hudu na kakar wasannin Bundsliga, Augsburg ta karbi bakuncin Mainz tare da shan kashi da ci uku da biyu.  An tashi canjaras biyu da biyu a wasa tsakanin Bochum da Holstein Kiel, yayin da Freiburg ta yi tattaki zuwa gidan Heidenheim ta lallasa ta da ci uku da nema. Union Berlin ta karbi bakuncin Hoffenheim ta kuma caskara ta da ci biyu da daya, yayin da Frankfurt ta karbi bakuncin Borussia Mönchengladbach ta kuma lallasa ta da ci biyu da nema. Wasan da aka fi ruwan kwallaye kuwa shi ne, wanda Bayern Munich ta bi Bremen har gida ta yi mata dukan kawo wuka da ci biyar da nema.

Victor Boniface na murnar kwallo na hudu da ya zuwa a kakar wasa ta banaHoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

Ita kuwa Bayer Leverkusen ta karbi bakuncin Wolfsburg ta kuma lallasa ta da ci hudu da uku, kana an tashi wasa tsakanin St.Pauli da ta karbi bakuncin RB Lepzig canjaras babu ci. Borussia Dortmund kuwa ta yi abin fada, bayan da ta yi tattaki zuwa gidan Stuttgart aka kuma yi mata ruwan kwallaye har biyar yayin da ta tashi da kwallo daya kacal. A yanzu haka dai Bayern ke saman tebur da maki 12, sai takwararta Bayer Leverkusen da Freiburg da Frankfurt da ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da na hudu da maki tara kowaccensu.

Manchester City na jan zarenta a Ingila

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, Manchester City ta yi kaka-gida a saman tebur da maki 13, duk da wasan da ta tashi canjaras biyu da byiu tsakaninta da kungiyar Arsenal da ke a matsayi na hudu da maki 11. Koda yake wasan ya so barin baya da kura, domin kuwa magoya bayan Arsenal na ganin da gangan alkalin wasa ya kara mintuna har 17 da a ganinsu shi ya bai wa City damar farke kwallonsu ta biyu. Kungiyoyin Leverpool da Aston Villa ne ke biye wa City a matsayi na biyu da na uku a saman teburin na Premier League.

Barcelona ta cera wa Real Madrid a Spain

Real Madrid ta Kylian Mbappe na a matsayi na biyu a teburin La ligaHoto: Gabriel Jimenez/AP Photo/picture alliance

A La Liga ta Spaniya, Barcelona ce a saman tebur da maki 18, inda ta bai wa babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid da ke a matsayi na biyu tazarar maki hudu. Koda yake a fafatawar Madrid din da RCD Espanyol Barcelona a karshen mako an samu cece-kuce, bayan da wasu ke ganin bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka bai wa 'yan Madrid din a mintuna na 90 na wasan da sabon dan wasanta Kylian Mbappé ya zura mata kwallo ta hudu a raga bai cancanta ba. Athletic Bilbao ce ke a matsayi na uku da maki 13, yayin da takwararta Atlético Madrid ke a matsayi na hudu da maki 12.

Ghana na da matsala da filayen kwallonta

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta janye wasu wasanni da aka shirya gudanarwa a Ghana, a filayen wasa na Baban Yara da ke birnin Kumasi saboda dalilai masu tarin yawa ciki da rashin ingancin filin wasa, kamar yadda wakiliyarmu Jamila Ibrahim Maizango ta sheda mana

Haddad Maia ta samu nasara a gasar tennis ta Koriya

Daria Kasatkina ta sha duka a hannun Beatriz Haddad Maia a wasan karshe na tennisHoto: Hasan Bratic/dpa/picture alliance

Bayan da ta sha kaye a gasar U.S. Open a wasan dab da na kusa da na karshe wato quarter-finals, fitacciyar 'yar wasan Tennis 'yar kasar Brazil Beatriz Haddad Maia ta samu nasarar lashe gasar Korea Open da ta ba ta damar daukar kofinta na farko a gasar Tennins ta duniya rukunin 'yan dai-dai. Ta dai samu wannan nasara bayan ta lallasa takwararta Daria Kasatkina 'yar kasar Rasha da ci daya da shida da shida da hudu da kuma shida da daya. Haddad Maia da ta gaza kai bantenta a wasan karshe a Seoul a shekara ta 2017, ta farfado da karfinta tare da samun nasararta ta farko a wannan shekara.

Musik....

Tseren keke na aksa da kasa ya dauki hankali a Switzerland

'Yan tseren keken da suka yi nasara a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics Remco Evenepoel da Grace Brown sun lashe gwajin maza da mata a gasar tseren keke ta duniya da Switzerland ta karbi bakunci. Yayin da 'yar Ostareliya mai shekaru 32 a duniya Brown ta lashe gasar a karon farko bayan da ta zo matsayi na biyu shekaru biyun da suka gabata, Evenepoel ya kare kambunsa ne. Mai shekaru 24 a duniyar dan kasar Beljiyam na ci gaba da taka rawa bayan da ya lashe kambun a gasar wasannin ta Paris Games. Ya samu nasara da dakika shida a gaban Filippo Ganna na Italiya, wanda shi ne dai ya zo na biyu a bara.