1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Labarin Wasanni; 27.12.2021

Mouhamadou Awal Balarabe MA
December 27, 2021

Wasannin lig-lig a Birtaniya ya ci gaba a lokacin Kirsimeti duk da cewa annobar corona na addabar kasar. CAF ta tsayar da ranar da kungiyoyi za su saki 'yan wasan da za su buga gasar nahiya da za a yi a Kamaru.

Großbritannien Huddersfiled | Fans mit Weihnachtsmützen
Hoto: Richard Sellers/PA Wire/picture alliance

Gasar kokawar gargajiya ta Nijar ta zo da mamaki, inda tun kafin a je ko'in aka fara waje road da 'yan wasan da ake ji da su.

Duk da cewa sama da mutum dubu 100 na kamuwa da corona a kowace rana a Birtaniya, hakan bai hana gudanar da wasannin da ake wa lakabi da Boxing Day da ke gudana a lokacin bukukuwan Kirsimeti ba. Sai dai an soke wasanni uku daga cikin tara ciki har da karawa tsakanin Liverpool da Leeds saboda 'yan kwallo da yawa sun kamu da COVID-19.

A wannan yanayin, Manchester City ta samu nasara a kan Leicester da ci 6-3 a wani wasa mai kayatarwa. Ko da shi ke kafin a tafi hutun rabin lokaci 'yan wasan koci Pep Guardiola na casa Leicester  4-0, amma abokan karawarsu sun yi nasarar farke kwallaye uku bayan da aka dawo fili daga. Sai dai kwallo Aymeric Laporte da bugun fenariti daga Raheem Sterling ya zira sun bai wa City damar yin rawar gaban hantsi. Amma Pep Guardiola bai yi mamakin yadda Leicester ta farka daga barci bayan dawowa hutun rabin lokaci tare da haifar wa kungiyarsa da damuwa ba.

A yanzu dai Manchester City tana cin karenta babu babbaka a teburin Premier lig inda take gaban Liverpool da maki shida har ma da Chelsea. Da ma dai ita Chelsea ta samu nasara a kan Aston Villa da ci 3-1 inda Jorginho ya zira kwallaye biyu yayin da Romelu Lukaku ya ci na ukun. Amma kungiyar da ta fi taka rawar gani a fada a wannan mako na 19 na premier lig ita ce Arsenal sakamakon ta lallasa Norwich da ci 5-0 da ta yi, lamarin da ya bata damar kusantar ukun farko a teburin gasar.

Ita kuwa Tottenham ta doke Crystal Palace da ci 3-0. Godiya ta tabbata ga kocinta dan Italiya Antonio Conte, wanda tun bayan zuwansa ba ta barasa da wasa ko daya ba. Amma a wani taron manema labarai, conte ya ce ba ya tsammanin cewa ci gaban zai dore.

A sauran sakamakon wasan na mako na 19 na Premier lig kuwa, Southampton ta ci West Ham 3-2 yayin da Brighton ta doke Brentford da ci 2-0. Kuma a daren yau, Newcastle da Manchester United za su yi wasan karshe.

A daidai lokacin da ya rage makonnin biyu a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka, hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta sanar cewa an ba 'yan wasa damar ci gaba da zama a kungiyoyin da suke bugawa har zuwa ranar 3 ga watan Janairu mai kamawa. Wannan matakin dai ya biyo bayan matsin lambar da kungiyoyin Ingila ke yi na son ganin 'yan wasansu da ke da tushe da Afirka sun gudanar da wasannin har zuwa karshen wannan shekara. Alhali bisa al'ada, ya kamata kungiyoyi su ba wa 'yan Afirka dama kwanaki 14 kafin a fara gasar a ranar 09 ga watan Janairu. Sai dai cikin wata wasika da FIFA ta aike zuwa ga kungiyar kulob din kwallon kafar Turai, ta ce an dauki wannan matakin ne domin nuna hadin kai ga kungiyoyin da abin ya shafa sakamakon yadda sake bullar cutar ta Covid-19 take dagula musu lissafi".

A makon da ya gabata ne, kungiyar ECA ta yi barazanar kin saki 'yan wasan Afirka da za a dama da su a AFCON, inda ta nuna damuwa game da ka'idojin kiwon lafiya da aka kafa sakamakon annobar corona. Sannan ta nuna hadarin da ke tattare da lokacin da dan wasa zai killace kansa bayan ya dawo gida kafin ya koma fagen atisaye.

Sai dai tuni wannan mataki na CAF ya fara haifar da illa ga kasashen da za su shiga gasar cin kofin Afirka, saboda akasarin 'yan wasansu ba za su sami damar gudanar da wasannin sada zumunta da aka shirya ba. Daga cikin kasashen da matakin ya shafa kai tsaya har da Senegal da Cote d' ivoire da Najeriya da kuma Maroko sobada kaso mafi tsoka na 'yan wasansu na bugawa ne a kasashen na Turai.

A Jamhuriyar Nijar, a daidai lokacin da aka shiga kwana ta hudu ta gasar cin takobin kokowar gargajiya karo na 42 a birnin Yamai, wasu daga cikin manyan ‚yan kokowa sun sha kasa a gasar ta bana wacce ta kunshin sabbin matasan 'yan kokowa. A jimlace dai zaratan ‚yan kokowa 80 daga jihohi takwas na kasar ne ke fafatawa a neman cin takobin na wannan shekara. kuma yanzu takobi na hannun jihar Tillabery, wanda ya sake azata a gasar da aka bude ta a rnar juma‘a da ta gabata.

Hoto: Lintao Zhang/Getty Images

Japan ta ce ba za ta tura jami'an gwamnatinta zuwa China domin wakiltar ta a Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing a watan Fabrairun 2022 ba. Duk da cewa ta ki amfani da kalmar kaurace wa gasar, amma Sakatare-janar na gwamnatin Japan Hirokazu Matsuno, ya nuna muhimmancin cewa kasar Sin ta mutunta 'yancin dan Adam tare da bin doka. Sai dai kasar Japan za ta tura Seiko Hashimoto, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Tokyo 2020 da aka gudanar a bazarar da ta gabata, da kuma shugaban kwamitin wasannin Olympics na Japan Yasuhiro Yamashita zuwa birnin Beijing domin wakiltarta.

Ita dai japan ta bi sahun kasar Amirka wajen juya wa China baya a wasannin olympik na lokacin bazara sakamakon musguna wa tsirara da abokan hamayya. sai dai fadar mulki ta Beijing ta yi alkawarin maida martani mai tsauri ga duk kasar da a cewarta take fakewa da wasanni wajen yin bita da kullin siyasa ko na diflomasiyya.

To masu bibiyar Labarin wasanni na Deutsche Welle, wannan shiri dai shi ne na karshe da muke gabatarwa a wannan shekarar kasancewar wannan ne Litinin na karshe na 2021. Muna alfahari da bibiyarmu da kuke yi a kowane lokaci, musamman ma irin korafe-korafenku da shawarwarin da kuke ba mu. Mun yi kokarin aiwatar da wasu daga cikin bukatunku kasancewa da bazarku ne muke taka rawa, saboda haka ne muka bibiyi muhummin lamaru da suka wakana a fagen wasanni a duniya musamman wasannin Bundesliga na jamus da muke kawo muku kai tsaye. A game da nahiyar Afirka ma ba a bar mu a baya ba, kama daga dakatar da shugaban hukumar CAF Ahmad Ahmad har i zuwa ga zaben sabon Patrice Montsepe. Sannan mun kawo muku sakamakon gasannin daban-daban ciki har da gasar yan wasan cikin gida na CHAN DA MOROKO TA LASHE; da yadda Al-Ahly ta Masar ta sake lashe gasar zakarun nahiyar Afirka, sai kuma uwa uba, yadda rikici ke dada mamaye hukumomin wasannin Najeriya da Kamaru, ko da shike Fecafoot an yi nasarar zaban Samuel Etoo a matsayin sabon shugaban hukumar.