1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 28.09.2026

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MA
September 28, 2026

Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun fara da kafar dama a wasannin share fagen shiga gasar AFCON ta badi. To sai dai muhawara ta barke a Najeriya kan amfani da 'yan wasan da aka haifa a Turai.

Fußball Afrika-Cup 2026 | Achtelfinale | Mali vs. Tunesien | Valery Yan und Djigui Diarra im Zweikampf
Hoto: Ulrik Pedersen/NurPhoto/picture alliance

Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun fara da kafar dama a wasannin share fagen shiga gasar AFCON ta badi. To sai dai muhawara ta barke a Najeriya kan amfani da 'yan wasan da aka haifa a Turai.

Jürgen Klopp ya kafa tarihin zama mai horas da 'yan wasan Jamus da ya jagoranci wasanni mafiya munin rashin tabuka komai bayan gaza nasara. Kwanaki biyu kacal bayan sanya ranar gwabza fafatawar da kowa ke mararin gani tsakanin shahararrun damben duniya Tyson Fury da Anthony Joshua, da alama baya ta haihu a kan wannan karon-batta.

Wasannin UEFA League:

Wasanni biyu ke nan sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jamus ya jagoranta, wadanda suka kasance masu dacin gaske gare shi da kuma Jamusawa, inda ya yi canjaras ci 1-1 da Netherlands, da kuma rashin nasara a hannun Girka har gida, dukkansu a wasannin gasar kasashen nahiyar Turai Uefa Nations League.

A watan Yulin da ya gabata ne Jamus ta nada Jürgen Klopp, bayan murabus din Julian Nagelsmann sanadiyyar shan kashi a hannun Paraguay, a zagaye na 'yan 32 na gasar cin kofin duniya da a ka gudanar a kasashen Amurka Canada da Mexico.

Da wannan sakamako, Jürgen Klopp ya kafa tarihin zama mai horaswa da ya fara da mafi munin sakamako a Jamus, tun bayan Sepp Herberger a shekarar 1937 da kuma Helmut Schön a shekarar 1965, wadanda suka yi kunnen doki a wasannin biyu na farko a jere.

UEFA Nations League 2026/27 | Taron manema labarai tare da Jürgen Klopp a Frankfurt.Hoto: Kai Pfaffenbach/REUTERS

Bayan ajiye tsohon zakaran duniya Cristiano Ronaldo a benci domin bai wa sabbin jini dama a wasan neman lashe kofin kasashen Turai, Portugal ta samu nasarar casa Norway da 2-1, ta hannun Joao Felix da kuma Goncalo Ramos, yayin da Norway ta rage jidon da kwallo tilo daga Erling Haaland.

Wasannin Kasashen Afirka AFCON 2027:

Najeriya ta fara wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON ta badi da kafar dama, bayan doke Madagascar da ci 2-1 a birnin Uyo, inda  mai horas da 'yan wasan Super Eagles Éric Chelle, ya gayyaci sabbin fuska da dama daga kasashen waje.

To sai dai masana kwallon kafa da wasu 'yan Najeriya na tantamar samun gina ingantaccciyar kungiya mai kishin kasa daga 'yan wasan da aka haifa a ketare, sakamakon sauyin yanayi na muhallin da suka taso a ciki da kuma karancin kishin asali.

Kwallon Tennis:

Jamhuriyar Czech ta lashe gasar Billie Jean King Cup, wadda aka gudanar karo na 12, bayan doke Ukraine.

Guje-guje da tsalle-tsalle:

'Yar wasan Habasha Tigst Assefa ta lashe gasar Berlin Marathon da aka gudanar ranar Lahadi, a cikin sa'o'i biyu da mintuna 11, to sai dai da kyar da jibin goshi ta tsallaka layin karshe sakamakon raunin da ta samu a lokacin da take gudun.

'Yar wasan, mai shekaru 29, ta taba lashe lambar azurfa a gasar Olympics ta birnin Paris shekaru biyu da suka gabata.

Dambe:

Kwanaki biyu kacal bayan da manyan zakarun damben duniya 'yan asalin Burtaniya Anthony Joshua da Tyson Fury suka amince da gwabzawa a ranar 11 ga watan Disamba mai zuwa, a birnin Cardiff na kasar Wales, fitaccen 'dan kasuwar nan na Amurka, kuma shugaban shirya damben duniya UFC Dana White, ya jefa tababa kan yiwuwar wannan karawa, lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin London, inda ya shaida musu cewa bai san ko za a yi wasan ko ba za a yi ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani