1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga: Dortmund da Hoffenheim sun ciri tuta

Mouhamadou Awal Balarabe ZUD(LMJ)
August 15, 2022

Manchester United ta dibi kashinta a hannu yayin da takwararta ta City ta mamaye abokiyar karawarta a Premier League. A Bundesliga kuma Dortmund da Hoffenheim sun zarta Bayern Munich kwazon zura kwallaye a mako na biyu.

Fussball 1. Bundesliga FC Bayern München Jamal Musiala
Hoto: Frank Hoermann/Sven Simon/IMAGO

A karshen mako ne aka gudanar da wasannin mako na biyu a gasar kwallon kafa ta Bundesligar Jamus. Borussia Dortmund da Bayern Munich da suka yi fice sun nuna bajinta a fafatawar: yaya-babba wato Bayern Munich ta doke Wolfsburg da ci 2-0, sakamakon kwallayen da Jamal Musiala da Thomas Müller suka zira.

Wannan nasarar ta bai wa Bayern Munich damar kasancewa a saman teburin Bundesliga da maki shiga, a gaban yaya-karama Borussia Dortmund,BVB, kungiya daya tilo da ita ma ta lashe wasanni biyu na farkon kaka.

Sai dai a wasansa da ke zama na farko a filin wasa na Allianz Arena, Sadio Mane ya ga ja da janye, inda aka soke duka kwallayen da ya ci sakamakon satar gida. Hasalima dai, wannan wasa na uku a hukumance a kakar bana ga Bayern, kuma na biyu a gasar Bundesliga, Mane ya sha caccaka daga marubuta wasanni biyo bayan karanci sarrafa kwallo a gaba. 

TERZIC Edin mai horas da 'yan wasa na DortmundHoto: Laci Perenyi/IMAGO

Ita dai BVB da Freiburg ta mamaye da ci 1:0 har zuwa minti na 77 da fara wasa, ta yi nasarar gasa wa abokiyar hamayyarta aya a hannu, inda 'yan wasan Dortmund uku Jamie Bynoe-Gittens da Youssoufa Moukoko da Marius Wolf da aka shigo da su suka zura kwallaye uku cikin minti15. Wannan nasara ce ta sanya aka tashi wasan 3-1, inda nasara ta tabbatar wa kocin Borussia Dortmund Edin Terzic cewa kungiyarsa tana da sabbin jini da za su iya cire ta a kanya a kodayaushe.

A halin yanzu dai Borussia Mönchenglach da ta yi kunnen doki da Schalke 04 2-2 ce ta kasance a matsayi na uku. Amma kuma a nata bangaren,  RB Leipzig na tafaiyar hawainiya, inda a karo na biyu a jere 'yan wasan koci Domenico Tedesco suka sake samun maki daya kacal bayan da aka tashi 2-2, lamarin da ya jefa ta a matsayi na 11. 

Babbar kungiyar ta biyu a Bundesliga da ke cikin mawuyacin hali ita ce Bayer Leverkusen, wacce a karo na biyu a jere ta dibi kashinta ci 1-2 a hannun FC Augsburg a gida BayArena. Abin takaicin ma shi ne: Leverkusen ta zama kurar baya da ita da VfL Bochum, wacce ita ma ta sake barar da wasanta na biyu a gaban Hoffenheim da 3:2.

Mai horas da 'yan wasan Hertha Berlin Sandro SchwarzHoto: Andreas Gora/dpa/picture alliance

A sauran wasannin kuwa: Hertha Berlin da Eintracht Frankfurt sun tashi ci 1-1, yayin da Mainz da Union Berlin suka tashi babu wanda ya ci wani 0-0. Sannan Werder Bremen da VfB Stuttgart sun rabu 2-2. 

A gasar La Liga ta Spain, inda aka gudanar da mako na farko, kungiyar Real Madrid wadda ke rike da kambun zakara ta yi nasara a kan Almeria da ci 2-1. Ita kuwa FC Barcelona ta tashi 0-0 da Rayo Vallecano, sakamakon kasa sarrafa damarmakin da ta samu duk da kasancewar Robert Lewandowski a fagen daga.  

A  gasar Serie A ta Italiya kuwa, gaba daya kungiyoyin Milan guda biyu sun kai labari, inda  AC Milan ta ci Udinese 4-2 yayin da Inter Milan ta lallasa Lecce 2-1. 

A gasar Premier League ta Ingila, an yi kare jini biri jini a  karawar da aka yi tsakanin Chelsea da Tottenham wanda aka tashi 2-2. Hasalima,karshen wasan ya kasance cikin tashin hankali, inda cacar baki tsakanin manajojin kungiyoyin biyu Thomas Tuchel da Antonio Conte ta rikide zuwa fada. A karshe dai an kore su daga filin wasan.

Sai dai Manchester United ta samu kanta cikin wadi na tsaka mai wuya a filin wasa na Brentfordt, inda aka casa ta da ci 4-0 . Amma takwararta Manchester City ba ta samu damuwa ba wajen lallasa Bournemouth da ci 4-0. Ita ma Arsenal ta yi nasara da ci 4-2 a kan Leicester, yayin da a nata bangaren, Liverpool za ta fafata da Crystal Palace.

Sabuwar gasar Super League mai rudani a Afirka

Biyo bayan kaddamar da gasar Super League da hukumar kwallon kafar Afirka ta CAF ta yi, masharhanta lamuran wasanni sun zaku don ganin makomar sabon zubi na gasar. Za a raba gasar zuwa rukunoni uku ne na kungiyoyi takwas da aka raba a yankuna (arewa, tsakiya-yamma da kudu maso gabas) tsakanin kungiyoyi 24 da suka fito daga kasashe 16 da zummar samar musu da karin kudin shiga . Sai dai wasu ma'abota kwallon kafa na ganin cewa Super lig za ta iya mummunan tasiri ko kyakkyawan tasiri ga sauran wasanni dabam-dabam na kwallon a daukacin nahiyar, kama daga Kofin Zakaru har zuwa Confederation Cup. 

Shugaban hukumar CAF Patrice MotsepeHoto: Weam Mostafa/Sports Inc/empics/picture alliance

Za a buga kakar wasan farko daga Agusta 2023 zuwa Mayu 2024 kuma Super League din ta Afirka za ta kunshi wasanni 197. 

Gasar Olympics a Jamus

Birnin Munich da ke kudancin Jamus na daukar bakuncin gasar wasanni tara da aka saba gudanar da su a gasar Olympics har zuwa 21 ga wannan wata na Agusta. Wannan ne dai gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle mafi girma a Turai da aka gudanar a jihar Bavaria tun bayan karbar bakuncin gasar Olympics shekaru 50 da suka gabata.

'Yan wasan 4700 ne suke kece raini na tsawon makwanni biyu, kuma karo na biyu na wannan gasar wasannin motsa jiki ta Turai da ake wa lakabi da Multi-Sport Championships. Kusan kasashe 50 ne ke wasa a  fannoni 12 domin samun lambobi 177.

'Yar tseren keke Letizia Paternoster 'yar kasar Italiya ta samu rauni bayan da ta fado a gasar tseren keke na Turai a birnin Munich a ranar Asabar. Baya ga wasannin motsa jiki dai, ana gudanar wasan tennis, da tseren kwale-kwale da hawan dutse duk da a gasar ta Olympics a Jamus.