1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Euro 2020: Wadanne kasashe ne suka haye?

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
June 28, 2021

Ta ware wa Portugal da ke rike da kofin Turai a gasar kwallon kafa ta neman lashe kofin nahiyarTurai, yayin da ta warware wa Jamhuriyar Chek da ke zama dan hakin da ka raina.

Euro 2020 - Gruppe B - Dänemark v Belgien
Thorgan Hazard ne ya zirawa Beljiyam kwallon da ta ba ta nasara a karawa da PortugalHoto: Hannah Mckay/REUTERS

Tafiya ta fara nisa a fafatawar da kasashe dabam-dabam ke yi na zuwa zagayen kusa da kusa da na karshe, a gasar neman lashe kofin kwallon kafa na nahiyar Turan. Daya daga cikin wasannin da suke fi daukar hankali shi ne karawa tsakanin Portugal da ke rike da kofin Turan da kuma Beljiyam da tauraronta ke haskawa. Sai dai kuma fitaccen dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo da 'yan uwansa sun dibi kashinsu a hannu a birnin Sevilla, inda Beljiyam ta doke su da ci daya mai ban haushi. A  wannan wasan mai cike da kalubale,  Portugal ta fi' Beljiyam samun damarmaki a gaban raga, amma Beljiyam ce ta yi nasarar zira kyakkyawan  kwallo sakamkon wani bugu daga Thorgan Hazard zuwa cikin raga, lamarin da Hazard ya danganta da kwallo mafi muhimmancin a cikin kungiyar kasarsa.

Italiya ta sha da kyar a karawarsu da OstiriyaHoto: Justin Tallis/REUTERS

A wasanta na gaba dai, Beljiyam za ta kara ne da Italiya wacce ta samu nasara a kan Ostiriya da ci biyu da daya. Ita dai Squadra Azzura ta Italiya wacce ta kayatar a wasanni rukuni tare da cin nasara uku a wasanni uku, gumin goshi ta kai labari domin kuwa sai da aka shiga karin lokaci ta doke Ostiriya ta David Alaba..Sai dai a nata bangaren kasar Netherlands ta fadi kasa warwas duk da rawar da ta taka a wasannin rukuni, inda Jamhuriyar Czech ta shammace ta da ci biyu da nema. Wannan sakamakon ya bayar da mamaki kwarai a gasar ta Turai. A wannan Litinin ne Croatia da Spain ke kece raini, yayin da Faransa da ke rike da kofin duniya ke karon batta da Switzareland. Ita kuwa Ingila za ta yi wasanta da Jamus, yayin da Sweden ke hamayya da Ukraine.

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahly ta Masar, na shirin lashe kofin champions lig karo na 10Hoto: Sports Inc/empics/picture alliance

Kungiyar kwallon kafar Al-Ahly ta Masar ta tsallake zuwa wasan karshe na neman cin kofin gasar zakarun Afirka, bayan da cikin sauki ta doke Esperance ta Tunisiya da ci uku da nema a mataki na biyu na wasan kusa da na karshe. Dama dai kungiyar ta birnin Alkahira ce ke rike da kambun zakarun nahiyar Afirka, kuma za ta yi kokarin lashe champions lig a karo na 10 cikin tarihinta, bisa gudunmawar da dan wasanta Mohamed Sherif da ya fi zira kwallaye a gasar ya bayar. A wasan karshen dai, Al Ahly za ta kece raini ne Kaizer Chiefs ta Afirka ta Kudu, wacce ta samu nasara a kan Wydad Casablanca ta Moroko da ci daya ada nema a karawar farko, kuma ta tashi canjaras babu ci a zagaye na biyu. A ranar 17 ga watan Yuli ne za a buga wasan karshe na kofin zakrun Afirka a filin wasa na Mohammed V da ke birnin Casablanca na Moroko.

A confederation cup kuwa na Afirka kuwa, wasan karshe zai hada kungiyoyi biyu da suka fito daga yankin Maghreb, wato Raja Casablanca ta Moroko da ta yi nasara a bugun fenariti a kan Pyramids FC da kuma JS Kabylie ta Aljeriya da ta doke Coton Sport ta Garouan Kamaru da uku da nema. Wannan dai shi ne karo na biyu da Raja Casablanca za ta yi kokarin lashe confederation cup baya ga na 2018, kuma za a buga wasan karshe a filin wasa na Cotonou da ke Jamhuriyar Benin a ranar 10 ga watan Yuli mai zuwa.