1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Ba bu barasa a gasar Katar

Suleiman Babayo LMJ
July 11, 2022

Halin da ake ciki a shirye-shiryen gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar Katar za ta karbi bakunci a karshen wannan shekara ta 2022.

Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya I 2022 Katar | Filin Wasan Al Thumama I Doha
Ba za a sayar da barasa a filayen wasanni ba yayin gasar kwallon kafa ta Katar 2022Hoto: Laci Perenyi/picture alliance

Yayin da shirye-shiryen gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniya da zai wakana a karshen wannan shekara ta 2022 da kasar Katar za ta dauki nauyi suka yi nisa, majiyoyi sun tabbatar da cewa ba za a sayar da barasa a harabar filayen wasannin ba. Za dai a gudanar da gasar a cikin watannin Nuwamba da Disambar wannan shekara da muke ciki, kuma an sanar da cewa a harabar filayen wasannin ne ba za a sayar da barasar ba amma za a sayar a wuraren da aka tanada gabanin wasanni da kuma bayan wasannin. Ba a daina haramta sayar da barasa a kasar ba, amma an tsagaita haramcin a gidajen giya da shagunan cin abinci. Sakamakon gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, an kara bude wurare na musamman na sayar da barasa. 

COVID-19, ta hana wasu 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea buga wasaHoto: Nick Potts/PA/empics/picture alliance

'Yan wasan tsakiya guda biyu na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, N'Golo Kante da Ruben Loftus-Cheek ba sa cikin wadanda za su bugawa kungiyar wasa lokacin wasannin sada zumunta a Amirka gabanin fara wasannin lig na Ingila da ake kira Premier League, saboda gwaji ya nuna suna dauke da cutar Covid-19. Dokokin Amirka sun hana duk wani wanda ba dan kasar ba shiga idan yana dauke da cutar ta Covid-19, sai dai bisa wasu dalilai na musamman ko kuma idan mutum ya yi riga-kafi a kalla sau biyu.

'Yar wasan Tennis Elena Rybakina ta kafa tarihiHoto: Javier Garcia/Shutterstock/IMAGO

Elena Rybakina ta zama 'yar kasar Kazakhstan ta farko da ta samu nasarar lashe gasar Tennis Ta Wimbledon da ake yi a Ingila duk shekara, bayan ta doke Ons Jabeur 'yar Tunisiya da ci uku da shida, shida da biyu da shida da biyu.  Ita dai Ons Jabeur ta kasance 'yar wasan Tennis mafi tasiri a nahiyar Afirka da kasashen Gabas ta Tsakiya, wadda a karshen watan Yunin da ya gabata ta kai matsayi na biyu a duniya tsakanin gwanayen wasan. Wannan nasara da Elena Rybakina 'yar shekaru 23 da haihuwa ta samu wajen lashe wannan gasar ta Wimbledon, ta sanya hakan ya zama karon farko da wani ko wata daga kasar ta Kazakhstan ya ko ta samu irin wannan nasara.