1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Duniyar wasanni a karshen mako

Suleiman Babayo LMJ
December 15, 2025

Wanne hali ake ciki game da wasannin lig na kasashen Turai? Lando Norris ya samu nasara a wasan tseren motoic da aka gudanar a Abu Dhabi. Kasar Norway ta lashe gasar cin kofin duniya na kwallon hannu na mata.

Bundesliga | 2025 | FSV Mainz 05 | Bayern Munich
Duk da canjarasa biyu da biyu da ta yi a gidan Mainz, Bayern Munich na saman teburHoto: Philippe Ruiz/Xinhua/picture alliance

Ba mu fara da wasannin Bundesliga na Jamus da aka kara a karshen mako, inda byan fafatawar da duka kungiyoyi suka yi, sakamakon ya kasance kamar haka. Har kawo yanzu dai duk da canjarasa biyu da biyu da ta yi a gidan Mainz, Bayern Munich ke saman tebur da maki 38 sai RB Leipzig a matsayi na biyu da maki 29. Borussia Dortmund na matsayi na uku ita ma da maki da 29, yayin da Bayer Leverkusen da Hoffenheim ke biye mata a matsayi na hudu da na biyar da maki 26.

Union Berlin 3, RB Leipzig 1

Monchengladbach 1, Wolfsburg 3

St. Pauli 2, Heidenheim 1

Hoffenheim 4, Hamburger SV 1

Leverkusen 2, Cologne 0

Freiburg 1, Dortmund 1

Bremen 0, Stuttgart 4

Fitaccen dan wasan Manchester City Erling HaalandHoto: Paul Currie/Shutterstock/IMAGO

Sannan a wasannin Premier League na Ingila kuwa kungiyar Manchester City ta bi Nottingham har gida ta doke ta 3 da nema, haka ita ma FC Fulham ta bi Burnley gida ta doke ta 3 da 2, yayin da Chelsea ta samu galaba kan Everton 2 da nema, ita kuwa Arsenal ta doke Wolverhampton 2 da 1. Kana Aston Villa ta bi West Ham gida ta doke ta 3 da 2. Har yanzu dai Arsenal ce a saman teburin na bana da maki 36, sai Manchester City na biye mata da maki 34 yayin da Aston Villa ke matsayi na uku da maki 33.

Barcelona na ci gaba da zama damaram a saman teburin La LigaHoto: Jose Breton/NurPhoto/picture alliance

A wasan La Liga da aka kara a Spaniya kuawa, kungiyar Barcelona ta doke Osasuna 2 da nema, yayin da Real Madrid ta bi Alaves har gida ta lallasa ta 2 da 1, kana kungiyar Mallorca ta doke Elche 3 da 1. Barcelona ce dai har yanzu a saman tebur da maki 43, yayin da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid ke biye mata da maki 39 sai kuma Villarreal CF a matsyi na uku da maki 35.

Gwarzon wasan tseren motoci na Abu Dhabi Lando Norris Hoto: Nicolas Economou/SportPix UK/IMAGO

A wasan tseren motoci na Formula 1 da aka kara a karshen mako, Lando Norris ya samu nasara a wasan da aka gudanar a Abu Dhabi. Yayin da shahararen mai tseren motocin Max Verstappen bai kasance a wajen wannan gasa ba sakamakon rashin lafiya amma, ya tura sakon taya murna.

'Yan matan Norway sun lashe gasar kwallon hannu ta duniya a banaHoto: Joel Marklund/BILDBYRÅN/picture alliance

Kasar Norway kamar yadda aka yi tsammani ta lashe gasar cin kofin duniya na kwallon hannu na mata a wata fafatawa mai zafi da kasar Jamus, inda aka tashi a wasan 23 da 20. Wannan ke zama karo na biyar da Norway take lashe gasar cin kofin kwallon hannu na duniya na mata, bayan karon batta da kasar Jamus.