1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Gasar Olympics ta birnin Tokyo

Suleiman Babayo LMJ
July 26, 2021

Gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya Olympics da ke gudana a birnin Tokyo na kasar Japan ta yi nisa, inda kasashe da dama suka samu lambabi.

Eröffnungsfeier Olympische Spiele Tokio 2020
Bikin bude gasar Olympics a birnin Tokyo, cikin matakan kariya daga coronaHoto: JEWEL SAMAD/AFP

A Jumma'ar da ta gabata aka bude gasar wasannin Olympics ta bana a birnin Tokyo na kasar Japan. Bikin bude gasar ya samu halartar manyan baki kusan 1000 kawai, saboda annobar cutar coronavirus da duniya ta samu kanta a ciki. Wasannin suna gudana a yanayi na dokar ta baci da aka sanya karo na hudu a yankin Tokyo baki daya, saboda dakile yaduwar coronavirus din. Firaminista Yoshihide Suga na Japan yana da fata kan wasannin na Olympics ba tare da 'yan kallo ba su gudana cikin nasara, duk da yanayin da ake ciki na annobar.  Kafin soma gudanar da shagulgulan bude taron da aka takaita, an yi tsit na minti guda domin nuna alhini ga miliyoyin mutane da suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronavirus din a duniya.

Kasashe da dama sun fara lashe lambobin yabo a gasar Olympics ta bana

Tuni dai aka fara lashe lambobi, inda Amirka ke kan gaba da lambobin zinare bakwai azurfa uku tagulla hudu jimilla 14. Yayin da Chaina ke matsayi na biyu da lambobin zinare shida azurfa uku da tagulla shida jimilla 15. A matsayi na uku akwai Japan mai masaukin baki wadda ke da lambobin zinare  shida azurfa daya da tagulla biyu, baki daya tana da lambobi tara ke nan. Ita kuwa Jamus kawo yanzu ta samu lambobin tagulla guda uku, kuma tana matsayi na 36 tsakanin kasashen duniya. 'Yar wasan Taekwando daga Tekiath Ben Yessouf daga Jamhuriyar Nijar ta samu nasara a wasan farko. Daga nahiyar Afirka, kasar Tunisiya kadai zuwa yanzu ta samu lambar yabo ta zinare daya da azurfa daya.