An kammala kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar
January 7, 2019A jamhuriyar Nijar a al'ummar jihar Dosso ta shirya kasaitaccen biki wajen tarben sabon sarkin kokowar Nijar Issaka-Issaka dan jihar ta Dosso wanda ya lashe takobin kokowar gargajiya na gasar karo na 40 da ta gudana shekarar bana a birnin Tillabery.
Yanzu kuma sai batun kwallo kafa a nan Turai kungiyar Barcelona ta zamo zakaran wucan gadi na gasar la Liga bayan da ta doke Kungiyar Getafe da ci biyu da daya. Dan wasan gaba na kungiyar ta Barcelona Leonel Messi ya fara ci wa kungiyarsa kwallon farko mintoci 20 da fara wasa.
Kungiyar ta Barcelona na ci gaba da jan zarenta a saman tebirin na La Liga da maki 40, Atletico Madrid wacce ta yi kunnan doki na daya da daya da Sevilla na a matsayin ta biyu da maki 35, Sevilla na a matsayin ta uku da maki 33 a yayin da Real Madrid wacce ta sha kashi a gida da ci biyu da babu a hannu Real Sociedad na a matsayin ta biyar da maki 30 wata tazarar maki 10tsakaninta da kishiyarta ta Barcelona.
Yanzu kuma sai nan kasar Jamus lokacin da 'yan wasan Bundesliga ke ci gaba da hutun sabuwar shekara, kafin komawa fagen daga a ranar 19 ga wannan wata na Janairu, kungiyar Bayern Munich ta ci shahararren dan wasanta dan asalin kasar Faransa Frank Ribery tarar kudi a bisa samunsa da laifin wasu zage-zage a saman shafinsa na Twiter, zage-zagen da Kungiyar ta ce sun saba wa dokokin da'a na kungiyar musamman daga babban dan wasan da ya kamata ya bayar da kyakkyawan misali. Sai dai Wasu jaridun kasar ta Jamus ma sun bayyana cewa hukuncin tara kadai ba zai wadatar ba ga laifin da dan wasan ya aikata inda suka bukaci da a dakatar da shi daga buga wa kungiyar wasa kwata-kwata.
Yanzu kuma bari mu leka kasuwar cinikin 'yan wasa inda a kasar Spain inda matashin dan wasan nan dan asalin kasar ta Spain Brahim Diaz wanda kontajinsa ke shirin kawo karshe a watan Yuni a kungiyar man City ya canza sheka zuwa Kungiyar Real Madrid a wani sabon kwantarji na tsawon shekaru shida a kudi miliyan 15 na Euro. a yayin da shi ma dan wasan Spain da ke buga wa Kungiyar Chelsea Cesc Fabregas ke shirin canza sheka zuwa kungiyar kwallon kafar kasar Faransa ta Monaco.
A wasannin Tennis na gasar gambizar maza da mata ta Hopman Cup ta kasar Ostareliya wacce aka kammala a karshen mako a birnin Perth gasar da ga al'ada ke zama ta bude kakar wasannin shekara na kollon Tennis. Jamus da Switzerland ne dai suka fafata a wasan karshe inda a bangaren maza zalla shahararren dan wasan kasar ta Swituerlanr Roger Federer dan shekaru 37 ne ya doke Alexander Zverev na Jamus mai shekaru 21 da ci 6-4, 6-2. sai dai a bangaren mata Angelika Kerber ta Jamus ce ta doke Belinda Bencic ta Switzerland ad ci 6-4,7-6,8-6. To amma a wasan gambizar maza da mata 'yan wasan kasar ta Switzerland Federer da Bencic sun lallasa Zverev da Kerber da ci 4-0,1-4, 4-3 nasarar da ta ba su damar lashe kofin na gasar ta Hopman Cup. Wannan shi ne karo na uku da Federer ke lashe wannan gasa ta Hopman Cup.
Bayan kammala wasannin mako farko na kallon na tennis a duiya, a bangare maza, Novak Djokovic dan kasar Sabiya ne zama na farko a duniyar kwallon tennis da maki 9135, Rafael Nadal dan kasar Spain na a matsayin na biyu da maki 7480, a yayin da Roger Federer ke a matsayin na uku da maki 6420. A bangaren mata kuma Simona Halep 'yar kasar Rumeniya ke a matsayin ta farko, Angelika kerber ta Jamus na bi mata a yayin da Caroline Wozniacki ke a matsayin ta uku a duniyar kwallon tennis ta mata.
Bari mu karkare shirin da gasar tseren motoci ta rairayi da aka fi sani da Rally Dakar wacce aka kaddamar a wannan Litinin a birnin Lima na kasar Perou. Motoci 334 da durobobi 541 ne za su halarci gasar ta tsawon kilomita dubu biyar daga ranar bakwai zuwa 17 ga wannan wata na Janeru. Wannan shi ne karo na 41 da ake gudanar da wannan gasar tseren motoci wacce a shekarar bana kuma a karon farko za ta gudana baki dayanta a cikin kasa daya. A shekara ta 1978 ne aka kaddamar a karon farko da wannan gasa wacce a wancan loakci ake kira Rally-Paris- Dakar da ke gudana daga wasu kasashen Turai zuwa wasu kasashen nahiyar Afirka. Sai dai tun a shekara ta 2009 wannan gasa ta koma a kasashen Latin Amirka.