1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
May 3, 2021

Borussia Dortmund ta samu kai wa ga wasan karshe a gasar cin kofin kalubale na Jamus bayan dukan fitar arziki da ta yi wa Holstein Kiel da ci biyar da daya. Najeriya na jan kafa wajen tinkarar wasannin Olympics.

DFB Pokal | Halbfinale | BVB vs Holstein Kiel | Tor (2:0)
Fafatawar Borussia Dortmund da Holstein Kiel a gasar cin kofin kalubale na JamusHoto: Friedemann Vogel/AFP/Getty Images

Masu iya magana kan ce makashin maza, maza ka kasheshi. Abin da ya samu kungiyar Holstein Kiel da ke a  rukuni na biyu na Bundesliga ta Jamus ke nan, inda makonni kalilan bayan nasarar yin waje road da Bayern Muncih a zagaye na biyu na gasar neman cin kofin kalubale na Jamus, Borussia Dortmund ta nuna mata rashin tausayi a wasan kusa da na karshe a ranar Asabar ta hanyar lallasa ta da ci daya bayan daya har biyar da nema. Biyu daga cikin kwallayen dai dan wasa Giovanni Reyna ya zira su, yayin da sauran ukun kuma aka same su daga Marco Reus da Thorgan Hazard da Jude Bellingham.

Wannan nasarar ta bai wa Borussia Dortmund damar ci gaba da yin mafarkin cika burinta na karshen kakar wasa a cewar Marco Reus: "Kamar yadda na fada sau da yawa a baya-bayan nan, babu sauran abin da ya rage mu yi face cin dukkan wasannin da za mu buga. Hakan zai ba mu damar zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. Kuma mu dawo da Kofin kwallon kafar Jamus zuwa gida Dortmund. Muna kan kyakkyawar tafiya, bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba, dole ne mu ci gaba da aiki tukuru, kuma za mu yi bita a karshen kakar wasanni ta bana."

Dortmund da Leipzig za su kara a wasan karshe na cin kofin kalubalen Jamus Hoto: Ronny Hartman/REUTERS

Wasan karshe na kofin kwallon kafar Jamus ko kuma kofin kalubale dai, zai gudana ne a ranar 13 ga wannan wata na Mayu da muke ciki, kuma Borussia Dortmund din za ta fafata ne da RB Leipzig, wacce ta jira har zuwa lokaci na karshe na karin lokaci wajen lashe wasa biyu da daya a gaban Werder Bremen a wasanta na kusa da na karshe. Hasali ma wasan na karshe zai zama dama ga mai horas da 'yan wasa na RB Leipzig Julian Nagelsmann wanda zai koma Bayern Muncih a karshen kaka, na lashe kofi kafin ya bar Leipzig. Kuma wannan shi ne abin da maigidansa Oliver Mintzlaff yake so: "Na gaya wa Julian cewa mun bar shi ya koma Bayern Munich, amma kafin hakan dole ne ya dawo da kofi gida. Ya san cewa matsin lamba na da yawa, amma ya yi nasarar shawo kan lamarin har ya cancanci zuwa wasan karshe. Mu yanzu za mu mayar da hankali kan wasanmu na Bundesliga, sannan za mu mayar da hankali kan wasan karshe a Berlin."

Kafin ma haduwarsu ta ranar 13 ga Mayu a babban birnin Jamus don wasan karshe na wannan gasar cin kofin Jamusanci karo na 78, Dortmund da Leipzig za su fara kece raini a ranar Asabar a wasan mako na 32 na Bundesliga. Ita dai Leipzig tana mafarkin lashe kofin Jamus a karon farko cikin tarihinta, yayin da Borussia Dortmund ke kokarin lashe DFB-Pokal a karo na biyar a tarihinta.

'Yan wasan nahiyar Afirka sun yi rawar gani a gasar gudun ya da kanin wani a PolandHoto: Ronald Zak/AP/picture alliance

'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na nahiyar Afirka sun taka rawar gani a gasar gudun ya da kanin wani ta duniya da ta gudana a karshen mako a  kasar Poland. Yayin da Kasar Afirka ta Kudu ta lashe zinare a tseren mita 4x100 na maza, su kuwa 'yan wasan Kenya sun samu azurfa a tseren 4x200m kuma sun kammala gasar a matsayi na biyu a tseren hadin gambiza 2x2x400m. Sai dai abin lura a nan shi ne, a bana an hana manyan kasashe kamar Amirka da Jamaica shiga gasar ta 2021. Su ma dai 'yan guje-guje da tsalle-tsalle na Tarayyar Najeriya ba su shiga wasannin na Poland ba, duk da muhimmancinsa wajen shirya gasar wasanin Olympic a birnin Tokyo na kasar Japan da ya rage kasa da watanni uku a fara gudanarwa. Maimakon haka ma Najeriya ta sanar da sauke dukkanin shugabanin gudanarwa na hukumomin wasanin motsa jiki da za su wakilci kasar bisa dalilai dabam-dabam ciki har da matsalar corona, abin da ya jefa damuwa a kan shirin da kasar ke yi na halartar gasar.

Daya daga cikin wasan tseren keke mafi shahara a nahiyar Afirka da ake wa lakabi da Tour du Ruwanda ya fara gudana a karshen mako a birnin Kigali. kwanaki takwas 'yan tseren za su shafe suna fafatawa kafin a san wanda zai  gaji dan Eritiriya Natnael Tesfatsion wanda ya lashe tseren karshe. Sai dai wani dan kasar Kwalambiya Brayan Sanchez ne ya zo na daya a matakin farko na tseren da ke zama irin sa na 13. 'Yan tseren keke da yawa ba su halarci wasan ba saboda matsalar annobar corona. Amma kuma ana damawa da shahararren dan tseren keke nan na Kanada James Piccoli da kuma tsoffin gwarzayen tseren guda uku ciki har da Joseph Areruya da Jean Bosco Nsengimana da Samuel Mugisha wadanda 'yan kasar Ruwanda ne. Wadanda suka shirya tseren keken sun dauki mahimman matakai domin hana yaduwar annobar ta coronavirus, inda aka yi wa daukacin 'yan tseren gwaji a lokacin da suka isa filin jirgin saman Kigali. Ita dai Ruwanda ta kasance 'yar takarar neman shirya gasar cin kofin duniya na tseren keke a 2025. A tarihin wasan tseren keke dai, nahiyar Afirka ba ta taba samun damar karbar bakuncin gasar duniya ba.