1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarun Afirka masu daukar hankali a Jamus

Usman Shehu Usman
September 27, 2024

Fara tace danyen man Najeriya a cikin kasar da matsalar rashawa cikin kudaden tallafin Turai zuwa Afirka, da kuma shirin kashe dubban giwaye a kasar Botswana sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Hoto: DW

Sharhunan jaridun Jamus na wannan mako zai fara ne da batun matatar man Dangote a Najeriya. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce Najeriya kasar da Allah ya hore wa arzikin man fetur a yanzu ta samu damar tace wa kanta man da take hakowa. Hamshakin dan kasuwa da ya kasance na farko a tattalin arzikin Afirka wato Aliko Dangote yana da burin ganin wannan matakin ya ba da damar bunkasa tattalin arzikin Najeriya, sai dai jaridar ta ce amma fa Aliko Dangote ya gamu da masu hamayya da wannan burin nasa.

Babban birnin Habasha na ganin wani gagarumin sauyi, wannan shi ne sharhin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta ce mazauna Addis Ababa na ganin irin rusau da ake yi, musamman wadanda ke zama a unguwannin marasa galihu. Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya kaddamar da gagarumin aikin sake wa birnin mai tarihi fasali, misali a wani bangaren tsakiyar birnin da ke da tarihi na dubban shekaru, a yanzu kusan an rusa komai da ke tsaye da sunan ginin gida ko offis. Wannan matakin dai ya kawo sanadin raba dubban mutane da da mahallansu.

Za mu dora da jaridar die Tageszeitung, wacce ta yi sharhi kan cin hanci da ke tattare da tallafin da Kungiyar Tarayyar Turai ke warewa don bai wa Afirka tallafi.  Jaridar ta ce tun daga shekara ta 2016 aka fara gano badakalar da ke tattare da kudaden tallafa wa Afirka. Tarayyar Turai dai na ba da biliyoyin kudi don tallafi a bangarori da dama a Afirka, amma ofishin kula da biciken kudi na EU, ya fidda wasu alkaluma da yawa da suke nuna cewa akwai bukatar tankade da rairaya kan yadda ake kashe kudin da EU ke aika wa Afirka don tallafi. Sai dai jaridar ta aza ayar tambaya cewar irin wannan bincike idan ya ci gaba to kuwa ba zai iya shafar wadanda ake bai wa agajin ba, domin ta yiwu a samu tsayawar ayyukan agaji a Afirka wadanda EU ke daukar nauyinsu.

Ita kuwa jaridar Bild Online cewa ta yi Botswana za ta harbe dubban giwaye. Da farko dai an shirya tura giwaye 20,000 zuwa kasar Jamus, amma kuma sabanin hakan yanzu an yanke shawarar cewa za a harbe giwayen. Jaridar ta kara da cewa, a yanzu wannan matakin na harbe giwaye maimakon aika su zuwa Jamus, Shugaba Mokgweetsi Masisi na kasar ta Botswana ya yanke shawarar a harbe su kawai. Masu kare mahalli ne dai suka yi ta sukar matakin abin da ake ganin ya sa ma'aikatar kare muhallin Jamus ta fasa karbar giwayen, ita kuwa Boitswana na neman dole yadda za ta yi da giwayen ganin yadda fari ke tinkarar kasar, wanda dole zai kai ga mutuwar dubban giwayen.