1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya: George Weah ya lashe zaben shugaban kasa

Yusuf Bala Nayaya
December 29, 2017

Al'ummar Laberiya na ci gaba da bukukuwa bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana George Weah a matsayin wanda ya lashe zabe zagaye na biyu.

Tsohon dan kwallon kafa kana sabon shugaban kasar Laberiya George Weah
Tsohon dan kwallon kafa kana sabon shugaban kasar Laberiya George WeahHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ana dai yi wa wannan zabe kallon wanda ya bude sabon babi a siyasar kasar ta Laberiya da ta ga tashe-tashen hankula a tarihinta. George Weah dan shekaru 51 a duniya ya girma ne a garin Clara da ke zama na marasa galihu a Monrovia babban birnin kasar. Ya kasance dan Afirka daya tilo da ya samu lashe kyautar lambar yabo ta dan wasan da ya fi iya taka leda a shekara, da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ke bayar wa. Kafin ya yi ritaya ya buga wasa a kulob din AC Milan ta Italiya da Paris St Germain ta Faransa da kuma kungiyar Chelsea ta kasar Birtaniya. Ya yi fice a harkokin siyasa tun a zaben shekara ta 2005, ya yi nasara a zagayen farko na zaben kafin daga bisani a zagaye na biyu Ellen Johnson Sirleaf wacce a yanzu za ta mika masa mulki ta kada shi. A shekara ta 2011 ya tsaya takrara mataimakin shugaban kasa, sai dai basu samu nasara ba.

 

Al'ummar Laberiya na murnar zaben George Weah a matsayin shugaban kasaHoto: Reuters/T. Gouegnon

A shekara ta 2014 ne ya samu nasarar zama dan majalisar kasa. A wannan karo kuwa ya kada Joseph Boakai wanda ke zaman mataimakin shugaban kasa mai barin gado. Shugaban hukumar zaben kasar Jerome Korkoyah ya bayyana cewa jam'iyyar CDC ta Weah ta lashe zaben da sama da kaso 56 cikin 100 yayin da jam'iyyar UP ta mataimakin shugaban kasa ta samu sama da kaso 38. A watan Janairun shekara ta 2018 mai zuwa ne dai  me zuwa ne dai George Weah zai karbi mulkin Laberiya daga hannun Ellen Johnson Sirleaf wadda ke zaman mace guda daya tilo da ta tba shugabancin kasa a Afirka. Wannan dai shi ne karo na farko da wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga awata a tsahon sama da shekaru 70 da kafa kasar ta Laberiya. Hakan dai ya sa 'yan kasar da dama da suka riski tarihi na yaki ke ganin wannan a matsayin wata dama ta ci-gaban da kasar ta samu a bangaren zaman lafiya. Tarihin Weah dai daga talaka zuwa mai arziki ya taka muhimmiyar rawa a irin farin jinin da yake da shi a kasar da ta gaji da shekaru 12 na mulkin Johnson Sirleaf da ya kawo karshen yakin basasa, amma kuma ya gagara yakar cin hanci da rashawa da ya gallabi kasar ta Laberiya, baya ga karuwar talauci a tsakanin al'umma. Duk da cewa masu adawa da tsarin Weah na cewa bai bada wasu tsare-tsare masu yawa ba da za su sa ya kai ga mulki, ana kallon zabar Jewel Howard-Taylor a matsayin mataimakiyarsa, wacce kuma mata ce ga tsohon jagora na fafatukar 'yanci kuma tsohon shugaban kasa Charles Taylor da ya yi ya taimaka masa wajen kai wa wannan matsayi.