1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya ta bukaci duniya tallafa mata kan cutar Ebola

Usman ShehuSeptember 16, 2014

Tun bullar cutar Ebola a kasar Laberiya, sai bangarorin kiwon lafiya suka tabarbare, don haka shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf ta bukaci kashen duniya su taimaka don ceto fannin kiwon lafiyan kasar.

James Gbata
Hoto: DW/Julius Kanubah

Kasar Amirka ta bayyana shirin tura dakarun soji zuwa yankin yammacin Afirka a yunkurin dakile cutar Ebola, yayin da shugabar Laberiyar take neman karin agaji daga kasashen duniya cikin harda Jamus.

Shugaban Amirka Barack Obama ya bayyana shirin na tura dakaru 3000 da gina cibiyoyi 17 na ba da magunguna, gami da horos da dubban ma'aikatan lafiya. Sojojin za su tabbatar da bin hanyoyin dakile cutar ta Ebola, mafi yawan sojojin za a tura kasar ta Laberiya wadda cutar ta fi tagayyara, da sauran kasashen Saliyo, da kuma Gini da ke yankin yammacin Afirka.

Tun farko Hukumar Lafiya ta duniya wato WHO ta ce ana bukatar ma'aikatan lafiya kwararru 500 zuwa 600 da ma'aikatan lafiya 'yan yankunan da aka samu barkewar cutar kimanin 10,000. Kasar Cuba ta amince da tura kwararru 165. Sannan kasar China ta tura ma'aikata wadanda za su rika ayyukan gwaji 59, dama tana da ma'aikata 115 da suke aiki a wani asibitin da China ke tafiyarwa.

Hoto: Getty Images

Shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta tura wasiku zuwa kasashen ketere, domin ganin karin taimako, inda Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kasance daya daga cikin wadanda aka aike wa da wasikar. Jakadiyar Laberiya a kasar ta Jamus Ethel Davis ta yaba da taimakon da Jamus ta bayar, amma ta ce ana neman kari, haka ke zama makasudin wasikar:

"Ana bukatar karin taimako, kamar yadda kuka sani cutar ba ta da magani, tana saurin yaduwa, cuta ce mai saurin tsallaka zuwa wata kasa. Idan kasashe masu karfi za su kara azama zai yi kyau. Saboda idan yau cutar tana Afirka ta yamma gobe babu wanda yasan idan za ta bulla."

Kungiyar Tarayyar Turai tana cikin masu tura wadanda za su bayar da horo wa ma'aikatan lafiya, da sauran tallafi a kasashen da aka samu bakewar cutar ta Ebola da ta hallaka fiye da mutane 2,400 daga cikin kimanin mutane 4,000 da suka kamu da cutar. Hukumar Lafiya ta Duniya, ta yi gargadi kan yadda cutar take yaduwa kamar wutar daji, a cewar shugabar hukumar Margaret Chan

Hoto: DW

"A kasashen uku da cutar ta fi ta'addi na Gini, Laberiya da kuma Saliyo ana samun sabbin kamuwa da cutar sosai, abin da ya fi karfi wuraren da aka ware domin cutar."

Wani abu shi ne taimakon da manyan kasashe kamar Jamus, ya kai mizanin da ake zato? Jakadiyar Laberiya a Jamus, Ethel Davis ta ce ba yabo ba fallasa:

"Suna ba da taimako ta hannun Hukumar Lafiya ta Duniya, wadda ita ce ke tsara yadda ake tunkarar cutar ta Ebola a yammacin Afirka. Ita kuma take duba kasashen uku da ke fama da cutar da kuma Najeriya da aka samu tsirarun masu dauke da cutar."

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana gab da shawo kan cutar a kasashen Najeriya da Senegal, amma zai dauki lokaci kafin dakile cutar ta Ebola a sauran kasashen uku na Laberiya da Gini da kuma Saliyo.

Mawallafi: Daniel Pelz/lSuleiman Babayo

Edita: Usman Shehu Usman