1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jam'iyyar Labourtana iya dawowa madafun iko

Suleiman Babayo AH
July 3, 2024

Kuri'ar sanin ra'ayin masu zabe ta nuna jam'iyya mai mulkin Birtaniya za ta sha kaye a zaben gobe Alhamis.

Muhawara tsakanin Rishi Sunak da Sir Keir Starmer
Firaminista Rishi Sunak na Birtaniya da Keir Starmer jagoran jam'iyyar LabourHoto: Phil Noble/dpa/picture alliance

Gobe Alhamis ake zabe kasa baki daya na Birtaniya inda ake sa ran a karon farko cikin shekaru 14 jam'iyyar Conservative za ta rasa madafun iko, inda Firaminista Rishi Sunak zai yi sallama da ragamar tafiyar da kasar, amma ya ce har yanzu yana da fata.

Karin Bayani: Rishi Sunak: Ruwanda tudun mun tsira ce

Lokacin zaben na Birtaniya ana sa ran jam'iyyar Labour mai matsakaicin ra'ayin gaba-dai gaba-dai za ta sake dawowa kan madafun ikon kasar, inda shugaban jam'iyyar Keir Starmer kana jagoran 'yan adawa zai zama sabon firaministan kasar. Shi dai Keir Starmer ya zagaya kasar lokacin yakin neman zabe kuma zai zama firaministan daga jam'iyyar Labour na farko tun bayan Gordon Brown wanda ya yi sallama da ragamar mulkin kasar ta Birtaniya a shekara ta 2010.