1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hare-haren Amurka kan Iran sun lafa

July 26, 2026

Ana fargabar karancin makamai da kayan kariya ya tilasta wa Amurka dakatar da kai wa Iran hare-hare.

Hare-hare Amurka kan Iran sun lafa cikin kwanaki biyu a jere
Hare-hare Amurka kan Iran sun lafa cikin kwanaki biyu a jereHoto: Thibault Camus/REUTERS

An shafe dare na biyu a jere ba tare da Amurka ta kai wa Iran hari ba, a daidai lokacin da wasu kafafen yada labarai na Amurka ke cewa akwai yiwuwar rundunar sojin Amurkar na fuskantar karancin wasu muhimman makamai bayan kusan watanni biyar ana gwabza yaki.

Duk da cewa a ranar Juma'a shugaban Amurka Donald Trump, ya yi bazanar kaddamar da hare-hare mafi muni kan Iran, amma an wayi garin Asabar da Lahadi ba tare jin karar fashewar bama-bamai ba, yayin da ita ma Teheran ta dakatar da kai wa kasashen yankin Gulf aminan Washington hare-hare.

Amurka na buba yiwuwar tsananta hare-hare kan Iran

A daidai wannan lokaci Jaridar New York Times, ta ambato wasu majiyoyi biyu masu masaniya kan lamarin, inda suka ce gwamnatin Amurka na nuna damuwa kan raguwar adadin makaman kariya da sauran kayan kare sararin samaniya da ake amfani da su wajen ba da kariya ga kasashen yankin Gulf daga makamai masu linzami da Iran ke harbawa a matsayin martani ga hare-haren Amurka. Jaridar ta kuma kara da cewa ana fargabar rikicin zai iya kara tsananta nan gaba.

Yaƙin Iran ya lakume wa Amurka $37.5b

Ita ma tashar CNN, ta ambaton wata majiya daga ma'aikatar tsaron Amurka, da ta shaida mata cewa a halin yanzu an dakatar da ayyukan soji kan Iran ne, saboda irin wadannan dalilai da New York Times ta ruwaito.