1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Lafiya Jari : 19.06.2026

Zainab Mohammed Abubakar AH
June 19, 2026

Tun bayan gano ta a shekarar 1976 a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, Ebola ta sake bayyana a karo na 17 a wannan kasa ta yankin gabashin Afirka.

Likitoci dauke da mai fama da rashin lafiyar Ebola a Kwango
Likitoci dauke da mai fama da rashin lafiyar Ebola a KwangoHoto: Anadolu Agency/IMAGO

A duk lokacin da aka ambaci Ebola, jama'a na fadawa cikin fargaba saboda halin da duniya ta tsinci kanta dangane bullarta a baya, kana kasancewarta annoba wadda galibi take kisa.  A cewar cibiyar kula da cututtuka ta Afirka dai, alamunta na zuwa da zazzabi mai tsanani, da ciwon jiki, da amai da gudawa, kuma tana yaduwa ta hanyar mu'amala kai tsaye da ruwan jikin mutanen da suka kamu da ita, ta gurbatattun kaya ko kuma mutanen da suka mutu sakamakon cutar.

Bizne wadanda suka mutu da Ebola a KwangoHoto: Anadolu Agency/IMAGO

Ma'aikatar lafiya ta Kwango ta ce a kullum ana samun karuwar sabbin mutane da suka kamu da cutar kuma ya zuwa yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai 782, ciki har da wadanda aka tabbatar sun mutu 181. Babban darektan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ana ci gaba da kokarin kaucewa karuwar yaduwar wannan cuta duk da cewa ana samun bullarta wajen yankin gabashin Kwangon inda ta fara bulla.(Daga kasa za a iya sauraron sauti)

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani