Lafiya Jari : 23.09.2025
September 26, 2025
Talla
A shekarun baya masu fama da ciwon da ke karya garkuwar jikin dan Adam wato Sida sun fuskanci mummunar kyama da tsongoma a tsakanin al'umma amma a kwana a tashi a yau da fadikarwa da gabatar da tsari na shan magani ya sa an kawo karshen tsongomar. Sai dai kalubalan da ke a gaban masu fama da ciwon na Sida a yanzu shi ne karanci magani da kuma yadda masu maganin gargajiya suka shiga sayar musu da maganin wanda ya haddasa hasar rayuka a Najeriya. Daga kasa za a iya sauraran sauti.