Ciwon mara na mata mai tsanani
July 22, 2022
Talla
Matan da shekarun su bai wuce jinin haila ba na fuskantar ciwo a kasan mararsu, kafin ko kuma a lokacin da jinin al'adar su ya fara zuba ko kuma bayan haka. Masana lafiya na bayyana cewa ciwon mara abu ne da ya zama ruwan dare kuma wani bangare ne na jinin haila da wasu mata ke samu. Irin wannan ciwon na kasan mara kan dauki kwana daya zuwa biyu ko uku ko fiye da hakan kwatankwacin yanayin yadda ya mace take. Yayin da wasu matan ciwon yake zuwa musu da tsanani akwai mata da yawa da ke zuwa musu da sauki .