1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lafiya Jari: Karuwar cutar koda a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AH
July 14, 2023

Najeriya na fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar koda wanda adadin da sannun a hankali yake karuwa fiye da yadda ake tsamani.

Hoto: Joe Carrotta/NYU Langone Health/AP/picture alliance

Yawan masu kamuwa da cutar koda a Najeriya ba zato ba tsammani, abin damuwa ne. Sama da mutane miliyan 20 ne yanzu haka a Najeriya ke fuskantar karuwar cututtukan koda yayin da miliyan 20 ke dauke da cutar. Duk da cewa mutanen bakar fata sun fi kamuwa da ciwon koda, wannan karuwa kwatsam a tsakanin 'yan Najeriya ciki har da matasa da kuma wasu lokuta yara na da matukar damuwa.