1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Lafiya Jari: Tasirin magungunan gargajiya

Muhammad Bello MAB
August 4, 2023

Magungunan gargajiya na samuwa daga bishiyoyi ko tsirrai wanda aka gada da kaka da kakanni. Amma zuwan Turanwan mulkin mallaka ya sa an rage amfani da su a kasashen Afirla sakamakon kawo magugunnan zamani.

Najeriya na cikin kasashen da ake amfani da magungunan gargajiyaHoto: DW/Z. Umar

Sana'ar sayar da magungunan gargajiya na cin karo da cikas sakamakon rashin kyakkyawan tsari, lamarin  da ke sa hukumomin wasu kasashen Afirka ciki har da Najeriya yin yi fito-na-fita da masu magungunan gargajiya sakamakon rashin bin ka'idoji da ke haifar da matsalolin kiwon lafiya. Ba safai ne masu magugunan gargajiya ke bayyana sirrin hade-haden tsirrai da suke yi ba.