1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lagarde ta gana da kwamitin tattalin arzikin Najeriya

Ubale Musa/ASJanuary 5, 2016

Christine Largarde da ke shugabantar Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) ta gana da kwamitin tattalin arzikin Najeriya da kuma 'yan kasuwar kasar.

Nigeria Lagarde bei Buhari
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A cigaba da ziyarar da shugabar Asusun Bada Lamuni na duniya IMF ta ke yi a Najeriya, Christine Lagarde ta yi wani zama na musamman da kwamitin da ke kula da tattalin arzikin kasar wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yomi Osinbajo ke jagoranta kana ta tattauna da 'yan kasuwar kasar daidai lokacin da ke neman mafita kan rikicin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Jami'ar dai tun da fari ta ce babu batun baiwa Najeriya bashi a cikin ajandarta ta zuwa Abuja sai dai ta ce IMF din na son ganin kasar ta samu sararin warware matsalolin da tattalin arzikin ta ke fuskanta. Daga cikin irin abubuwan da ta lissafa da za su taimakawa kasar fita daga wannan kangi kuwa har da taka-tsantsan wajen kashe kudade. Lagarde din ta ce ''za mu yi farin cikin samar muku da kwarrarun shawarwari. Kuna bukatar cibiyar haraji mai kwarin gaske da hukumar bashi mai karfi da kuma hukumar tara kudin fito''.

Babban bakin Najeriya na son a samo hanyoyi na warware matsalar tattalin arziki a Najeriya

Baya ga zaman da ta yi da jami'an gwamnati, shugabar hukumar IMF din ta share tsawon sa'o'i biyu ta na wata ganawar sirri da 'yan kasuwar kasar kana da safiyar Larabar nan (06.01.2016) za ta tattauna da gwamnan babban bankin kasar har ila yau an tsara Lagarde din za ta gana da shugabannin bankuna masu zaman kansu da kuma hukumomi da cibiyoyi na gwamnatin da ke da ruwa da tsaki da batu na kudi.