1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar EU ta zabi Lagarde shugabar ECB

Abdullahi Tanko Bala
September 17, 2019

Zaben da 'yan majalisar dokokin Turai suka yi wa Christine Lagarde ya share mata fagen zama mace ta farko da za ta shugabanci babban Bankin tarayyar Turai ECB

Christine Lagarde
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Woitas

Majalisar dokokin Turai a wannan Talatar ta bada cikakken goyon baya inda suka zabi Christine Lagarde tsohuwar shugabar asusun bada lamuni na duniya domin zama shugabar bankin Tarayyar Turai a nan gaba.

A watan Julin da ya gabata ne aka gabatar da sunan Lagarde domin maye gurbin shugaban Bankin Turan Mario Draghi masanin tattalin arziki dan kasar Italiya.

A kuri'ar suka kada 'yan majalisa 394 suka amince da zabin Lagarde yayin da 206 suka kada kuri'ar rashin amincewa  sai kuma 'yan majalisa 49 wadanda suka kaurace wa zaben.

Ana sa ran shugabannin kasashe Turai za su tabbatar da zaben Christine Lagarde a taron kolin da za su gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Oktoba.

Idan an tabbatar da nadin na ta za ta kasance mace ta farko da za ta shugabanci babban Bankin na tarayyar Turai.