Lai Mohammed: Ba ma tauye 'yancin addini
December 8, 2020
Talla
Ministan yada labaran kasar Lai Mohammed a cikin sanarwar da ya fitar ya ce Najeriya ba ta tauye wa kowa ‘yanci na gudanar da addini ba, kuma rashin tsaro ya shafi dukkan mabiya addinan da ke kasar. Kazalika ya ce kasar za ta ci-gaba da kare 'yancin addinin kowa kamar yadda kundin tsarin kasar ya tanadar. Wannan martanin dai na zuwa ne bayan da kasar Amirka ta sanya Najeriyar cikin jerin sunayen kasashen da ke hana walwalar addini.
sai dai wani lauya da ke da rajin kare hakkin bil Adama a Abuja Frank Tietie ya yaba wa rahoton na Amirka, inda ya ce mabiya addinai marasa rinjaye na fuskantar wahalhalu a kasar.