Laifukan yaki a rikicin Sudan
December 3, 2025
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun zargi mayakan rundunar RSF na Sudan da alikata laifukan yaki sakamakon hare-haren da suka tarwatsa mutane da dama a lardin Darfur. Mayakan sun karbe da yankin inda suka aiwatar da ta'asa a garin el-Fasher.
Yanayin da ake ciki
Kungiyar Amnesty International ta fitar da rahoton da ya nuna yadda mayakan na RSF ke halaka fararen hula da garkuwa da su, gami da lalata makarantu da asibitoci gami da wuraren ibada na mutane. Kungiyar ta kasa ta kasa ta bukaci gudanar da bincike domin hukuntan wadanda suke da hannu a cikin wannan laifuka na yaki.
Watanni 30 aka kwashe ana kai ruwa rana tsakanin mayakan na RSF da sojojin gwamnatin Sudan, inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka tabbatar da mutuwar dubban mutane, yayin da fiye da milyan 14 suka tsere daga gidajensu.