Laimar PDP ta fara nadewa
April 8, 2015 Babu dai zato ba kuma tsammani aka kai ga zuwa karshen hakuri na shugaban kasar, da ke ikirarin zama gwarzo na demokaradiyyar Tarayyar Najeriya, amma kuma yake kukan cin mutunci na magoya baya da jami'ai na gwamnati.
Kakakin shugban Reuben Abati dai, yace shugaban kasar ya damu kwarai da yanda wasu da ya kira masu kokari cika buri na siyasa ke amfani da sabuwar nasarar adawar kasar ta Najeriya, da nufin musgunawa jami'ai na gwamnatin kasar da ke shirin barin gado
“Shugaba Jonathan ya yi Allah wadai da kokari na musgunawa jami'ai na gwamnatinsa, kuma ya bukaci duk wadanda abun ya shafa da su ci-gaba da ayyukansu, ba tare da wani tsoro ba. Shugaban kasar dai ya yi gargadin cewar, wannan lokaci ne na hadin kai da nufin tabbatar da ci-gaban kasa, amma ba lokaci na ramuwar gayya ko kuma anuna kabilanci ba. Gwamnatin tarayya ba za ta lamunci duk wani kokari na tada hankali da nufin cika buri na siyasa ba”
Duk da cewar dai Jonathan din bai fito fili domin karin haske bisa matakin da ya ke kallo da kamanni na musgunawar ba, kama daga jihar |Ekiti inda tasku ke zaman karatun gwamnan jihar kuma jagora ga goya baya ga Jonathan, ya zuwa ragowar jihohi inda sauyin sheka ya zamo sabon salo na yayan jam'iyyar PDP mai mulki. Daga dukkan alamu dai tana kara baki da duhu ga jam'iyyar da ta share shekara da shekaru ta na fada ana amsawa a kasar.
To sai dai kuma a fadar Alhaji Umar Dembo da ke zaman shugaban kungiyar magoya baya ta Buhari, rikicin Ekitin bai isa jam'iyyar PDP dama shi kansa shugaban kasar nunin yatsa ya zuwa APC.
“Mutun nawa PDP suka cire a irin wannan a lokacinsu. Sai dan mun zo. Mutane na da damarsu da ikonsu da kuma aikinsu in suna so su yi to za su yi. Ai PDP sun sha tsige gwamnoni ta irin wannan, ance sun yi ba daidai bane. Gafiya ce kawai ke son tsira dana bakinta”
Kokarin tsira da mutunci ko kuma karba a jiki na irin ayyukan da ka shuka dai, tuni tsamanni ya yi nisa a tsakanin al'ummar kasar na bincike, dama tabbatar da kwato kaddarori na kasa daga hannun jami'an da ke shirin barin gadon a halin yanzu.
Abun kuma da a tunanin Garba Umar Kari da ke zaman masharhanci na siyasa ta kasar da kamar wuya, ya kai ga samuwa ga Jonathan da magoya bayansa cikin sauki.
“Ko da shugaba Jonathan ya zauna ina ga manyan jami'ansa da makarrabansa ba za su zauna lafiya . In kuma suka zauna to 'yan kasa dama kasa da kasa za su ga sabuwar gwamnatin Buhari, ba da gaske take ba. A fili take an yi facaka da kukdade, an kuma sace su. Kuma abun da mutane ke son gani kawai shi ne dawo da kudaden”
Abun jira a gani dai na zaman mafita ga gwamnatin da ke da dan kashi a gindinta, amma kuma ke neman hanyar zuwa gida domin hutawa.