1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hare-haren Lakurawa a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
December 18, 2024

A Jamhuriyar Nijar yanayin kan harkokin tsaro da ke ci gaba da rincabewa inda wannan sabon gungu na 'yan ta‘adda da ake kira Lakurawa ke yawaita kai hare-hare a wasu yankunan Jamhuriyar Nijar da ke da iyaka da Najeriya.

Sojojin Jamhuriyar Nijar
Sojojin Jamhuriyar NijarHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Wanan matsala ta tsaro dai da ke wakana a wasu sass ana jamhuriyar Nijar musamman ma a yankin iyakokin Sokoto da Kebi da ke Tarayyar Najeriya, ga masu lura da al'amuran yau da kullum da basu basu da saurin mantuwa sun ce daman sun sa a rina domin kuwa dun da jimawa hukumomin Nijar sun sanar da wata manakisa da ake kitsawa inda jami'an wasu kasashe da ba na Afirka ba ke sintiri na zuwa da zowa a wasu yankuna dake makwabtaka da kasart ta Nijar wanda suke ganin daman sakamakon shine wannan da ya haifar da wasu yan bindiga da ake kira lakurawa.

Karin Bayani: Sojan Nijar sun yi artabu da Lakurawa a iyaka da Najeriya

Sojojin Jamhuriyar NijarHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

A nazarin na masanin harkokin tsaro Farfesa Dicko Abdourahamane, ko ficewar Nijar, Mali da Burkina faso daga ECOWAS tare da neman cin gashin kansu lamari ne da ka iya haifar wannan kasashe tashe-tashen hankula daga wadanda ke da adawa da wannan tsari na ciki da wajen kasashen. Tuni dai daman a wani taron Majalisar Ministoci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da wasu kudirin da ta dauka na gina kananan filayen tashi da saukar jirage a yankunan da bututun man fetur ya bi don daukan matakin gaggawa da zaran an samu labarin wata matsala ko kuma yin rigakafinta amma kuma kafin wannan mataki abin jira shi ne matakin gaggawa da hukumomin na Jamhuriyar Nijar da Najeriya za su dauka domin magance matsalar da ke neman saka halin zaman dar-dar a tsakanin wadannan al'umomi makwabtan juna na Nijar da Najeriya da kuma kasar Jamhuriyar Benin.