Laluben hanyoyin warware rikicin Gabas ta Tsakiya
August 9, 2013A mako mai zuwa za a koma teburin shawara tsakanin Isra'ila da Palestinu, bisa shiga tsakanin Amurika.
Jennifa Psaki kakakin ofishin Sakatariyar Harkokin wajen Amurika da ta bada labarin, ta yi karin haske:
ta ce:Za a koma Tattanawa tsakanin Isra'ila da Palestinu ranar 14 ga watan Ogusta a birnin Qudus, sannan kuma daga bisani a shirya wani taro a Jericho.Babban jikadan da Amurika ta wakilta a wannan tattanawa, Martin Indyk zai halarci taron.
Jennifa Psaki ta ce, za su amfani da wannan dama, domin dora duk matsalolin da ke hana ruwa gudu a kan tebur, da zumar samar da hanyoyin warware su.
Tun shekara 2010, aka watse baran-baran, tsakanin bangarorin biyu masu gaba da juna.
Sai karshen watan Yuli da ya gabata su ka sake ganawa a birnin Washington, bisa shiga tsakanin Sakataran Harkokin wajen Amurika John Kerry.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu